Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan Kano ta kori Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP ta bayyana jam’iyyar APC da Dan takararta Dr. Nasiru Gawuna a matsayin wadda ta lashe zaben da aka yi ranar 18 ga watan Maris.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana Yusuf wanda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar (NNPP) a matsayin wanda ya lashe zaben.
Yayin da Nasir Gawuna, abokin hamayyarsa na APC bayan ya taya shi murna jam’iyyarsa ta garzaya kotu.
Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Gombe da ta yi zamanta a Gombe, a ranar Talata, ta yi watsi da nasarar zaben shugaban majalisar dokokin jihar, Hon. Abubakar Leggerowo.
Idan za a iya tunawa dai an zabi shugaban majalisar ne a karkashin jam’iyyar APC mai mulki don wakiltar mazabar Akko ta tsakiya a majalisar dokokin jihar sai dai kuma babban abokin hamayyarsa a zaben, Alhaji Bashir Abdullahi, na jam’iyyar PDP. ya kalubalanci nasarar da ya samu a kotu.
Kotun karkashin mai shari’a Michael Ugar ta soke zaben shugaban majalisar ne saboda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta soke kuri’un da aka kada a wasu rumfunan zabe a mazabar wanda mai shigar da kara ya koka da shi a gaban kotun cewa matakin ya bai wa wanda ake kara nasara da ba ta dace ba a zaben ranar 18 ga Maris, 2023.
Mai shari’a Ugar ya yanke hukuncin cewa soke sakamakon zabe mai lamba 001, 024 da 014 na Kumo ta Gabas a karamar hukumar Akko a jihar an yi kuskure tare da ba INEC umarnin ta sake gudanar da zabe cikin kwanaki 30 masu zuwa don tantance ainihin wanda ya lashe zaben kujerar majalisar.
Sai dai kakakin majalisar Leggerowo ya nuna rashin gamsuwa da hukuncin da kotun ta yanke kuma ya sha alwashin daukaka kara a gaban kotun daukaka kara cikin gaggawa.
Source: LEADERSHIP HAUSA