Kotun kolin Nijeriya ta sanya ranar Alhamis domin yanke hukunci kan karar da ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da na jam’iyyar Labour (LP), Peter Obi suka shigar na kalubalantar sakamakon zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu wanda ya bayyana shugaba Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa.
Daraktan yada labarai na kotun kolin, Dr Festus Akande ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
A ranar 6 ga watan Satumba ne kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta yi watsi da karar da PDP da LP suka shigar gabanta kan rashin gamsashshiyar shaida, amma take Obi da Atiku suka daukaka kara.
A wani labarin na daban kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Adamawa za ta yanke hukunci kan karar da ‘yar takarar jam’iyyar APC, Aishatu Dahiru Binani ta shigar, inda ta ke kalubalantar nasarar Gwamna Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP a 28 ga watan Oktoba, 2023.
Idan dai za a iya tunawa, jam’iyyar APC da ‘yar takararta ne suka shigar da kara kan ayyana Gwamna Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.
APC ta yi zargin karya dokokin zabe da kuma tafka magudin zabe. APC da Binani a cikin kokensu, sun bukaci kotun ta tabbatar da sanarwar da kwamishinan zabe na jihar, Hudu Yunusa Ari ya yi wanda ya ce, APC ce ta lashe zaben.
A bangaren Jam’iyyar PDP da dan takararta, Fintiri, sun gabatar da bukatarsu a gaban kotun inda suke neman kotun da ta yi watsi da karar da APC da ‘yar takararta suka shigar.
Source LEADERSHIPHAUSA