Kotun Daukaka Kara ta shirya tsaf don yanke hukunci kan karar da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya daukaka a gobe Juma’a 17 ga watan Nuwamba 2023 da karfe 10 na safe a Abuja.
Hakan na kunshe ne acikin wata Sanarwa da wani mataimaki na musamman kan yada labarai na Kwankwasiyya, PA Ibrahim Adam da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna Abba Kabir Yusuf suka rabawa manema labarai.
Wannan rana dai, ta kasance muhimmiya wacce al’ummar jihar Kano suka dade suna tsumayi.
In ba a manta ba, a baya kotun sauraron kararrakin zabe da ke zamanta a Jihar Kano ta kwace kujerar Gwamna Abba Yusuf na NNPP ta baiwa Nasir Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin halastaccen Gwamna jihar.
A wani labarin na daban akalla mutane biyu ne aka tabbatar da mutuwarsu tare da lalata gidaje fiye da 1000 bayan da wata gobara ta tashi a sansanin ‘yan gudun hijira na Muna Alamdari da ke Maiduguri a jihar Borno a ranar Laraba.
Gobarar wacce ta tashi da misalin karfe 6:00 na safe, ta shafe sama da awa daya kafin jami’an hukumar kashe gobara ta jihar su shawo kanta.
Darakta-Janar na Hukumar bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar, Dokta Barkindo Muhammad, wanda ya tabbatarwa manema labarai afkuwar lamarin, ya ce, rundunar hadin guiwa ta farar hula, da hukumomin tsaro, da wasu nagartattun ‘yan kasa ne suka taimaka wajen kashe gobarar.
Barkindo ya ce, hukumar ta fara tantance irin barnar da gobarar ta yi don fara shirin bayar da agajin gaggawa ga wadanda abin ya shafa.
“Mun fara samar da buhunan shinkafa 500, barguna da sauran kayayyaki domin rage musu radadin wahalhalu,” in ji shi.
Source: LEADERSHIPHAUSA