A wannan makon ne dai kotun kolin Nijeriya za ta saurari kararraki 21 da suka shafi rigingimun zaben gwamnoni da aka gudanar a jihohin Nijeriya.
kararrakin da za a ci gaba da saurare sun haɗa da jihohin Ebonyi da Plateau da Delta da Adamawa da Abia da Ogun da Cross River da Akwa Ibom, daga ranar Litinin zuwa Alhamis.
Kazalika, kotun na iya yanke hukunci kan kararrakin zabukan Kano da Legas a ranar Juma’a.
Jadawalin kotun na ranar Litinin din da ta gabata ya hada da daukaka kara guda daya na jam’iyyar APGA, biyu na jam’iyyar PDP da dan takararta, Chukwuma Odii Ifeanyi da kuma kararraki biyu na jam’iyyar APC da dan takararta na jihar Benue.
A ranar Juma’a ne ake sa ran kotun za ta yanke hukunci, inda za ta kammala ayyukan makon, musamman ma a kararrakin zaben gwamna da aka yi a baya, kuma ana sa ran za a ƙarƙare satin da jihon Legas da Kano.
A wani labarin daya gabata dai damayau Kotun kolin Nijeriya da ke Abuja ta fara sauraren karar zaben gwamnan Kano da Gwamna Abba Kabiru Yusuf da Jam’iyyar NNPP da INEC suka shigar gabanta.
Ma su shigar da karar suna kalubalantar hukuncin kotun sauraren karar zaben gwamnan Kano da Kotun daukaka kara suka ayyana dan takarar Jam’iyyar APC, Dr. Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano.
A zaman na yau, tunda farko Kotun ta ce, ba ta da lokacin sauraren ƙarar NNPP da Abba da INEC da suka shigar gabanta har guda tara (9), sai dai su zaɓi guda ɗaya acikin taran.
Daga bisani kotun ta ba ma su ƙara da wanɗanda ake ƙara minti 10 kan kowane bangare ya faɗi matsayarsa. Lauyoyin APC da NNPP duka sun gabatar da jawabansu a gaban kotu.
A nasa jawabin Lauyan INEC, ya gabatar da bayyanai kan tanadin da dokar zaɓe ta yi kan kuri’un zaɓe marasa satamfi da sa-hannu da kwanan wata.
Yayin zaman shari’ar na yau Kotu ta gamsu takardun shari’a na kotun ɗaukaka ƙara na farko cewa kuskure ne, ta kuma karɓi takardu na biyu bayan da kotun ta gyara kuskuren da ke jiki.
Cikin tambayoyin da Kotu ta yi wa Lauyan hukumar zabe ta INEC ta tambaye shi shin ko waɗannan ƙuri’un zaɓen naku ne (Marasa satamfi da sa-hannu da kwanan wata)? Sai Lauyan INEC ya amsa da Eh ƙuri’unmu ne (bana bogi bane).
Daga bisani Kotu ta yi ƙarin haske kan batun satar ƙuri’un zaɓe a Nijeriya, wanda ta ce wajibi ne doka ta yi aiki don magance matsalar ba a iya Kano kaɗai ba a duk faɗin Nijeriya, saboda wajibi ne kiyaye doka da oda.
A karshe Kotun ta kammala sauraron ƙarar, ta kuma ce za ta sanar da ranar yanke hukunci kan shari’ar.
Source: LEADERSHIPHAUSA