Wata babbar kotu a Najeriya ta yi watsi da karar da wasu mutane suka shigar, inda suke kalubalantar tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar a matsayinsa na dan kasa.
Rahotanni sun ce, wata kungiya da ake kira EMA ta gurfanar da Atiku a kotu tare da jam’iyyarsa da hukumar zabe da kuma babban lauyan kasa, inda ta ce tsohon mataimakin shugaban kasar ba dan Najeriya ba ne ta hanyar haihuwa, saboda haka ba shi da hurumin tsayawa takarar zabe.
Masu gabatar da karar sun bukaci kotun da ta yi amfani da sashi na 25 da 131 na kundin tsarin mulki domin hana Atiku tsayawa takarar zaben shekara mai zuwa.
EMA ta ce lokacin da aka haifi Atiku, yankin da ya fito na Jihar Adamawa na cikin yankin Arewacin Kamaru ne amma ba Najeriya ba.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewar, kafin watsi da karar gwamnatin jihar Adamawa ta bukaci sanya ta cikin shari’ar, inda ta jaddada sahihancin Atiku na tsayawa takarar zaben shugaban kasar da za a yi.
Gwamnatin ta bayyana Atiku a matsayin cikaken dan kasa wanda ya tsaya zabe aka kuma zabe shi a matsayin gwamna da mataimakin shugaban kasa.
Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta tsayar da ranar 26 ga watan Maris na wannan shekara domin gudanar da taronta na kasa domin zaben shugabannin da za su jagorance ta.
Da farko dai, sanarwar da jiga-jigan jami’iyyar suka fitar a yau Litinin ta ce, an fasa gudanar da taron har sai baba-ta-gani.
Wannan na zuwa ne bayan rahotanni daga Abuja sun ce, gwamnonin jam’iyyar sun gudanar da taro domin dinke barakar da aka samu da kuma matakan da suka dace wajen sasanta ‘yayan jam’iyar da aka batawa lokacin da aka gudanar da zaben shugabanni a matakan jihohi.
Wasu daga cikin ‘yayan jam’iyyar sun yi barazanar zuwa kotu domin kalubalantar shugabannin rikon saboda abinda suka kira gazawar da suka yi na shirya taron kasa domin zaben shugabannin gudanarwar jam’iyyar tasu.
Masu sanya ido akan siyasar Najeriya na kallon wadannan matsaloli a matsayin zakaran gwajin dafi ga jam’iyyar mai mulki musamman ganin yadda aka samu rarrabuwar kawuna a tsakanin ‘yayan ta a daidai lokacin da ake shirin tinkarar zaben shekara mai zuwa.