Babbar kotu tarayya da ke Abuja, ta yi watsi da karar da wasu mazauna birnin suka shigar a gabanta suna neman ta hana rantsar da shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu.
Yayin da yake yanke hukuncin a ranar Talata, alkalin kotun, mai shari’a Inyang Ekwo, ya umarci masu karar da kowannensu ya biya Naira miliyan 10 ga ministan shari’a kuma Atoni-Janar na kasa.
Masu karar dai na ikirarin cewa shugaba Bola Tinubu bai samu samu kashi 25 cikin 100 na kuri’un da aka kada a baban birnin tarayyar Abuja.
Don haka suke ganin bai cancanci zama shugaban kasar nan ba.
Mai shari’a Ekwo ya ce masu karar ba su da ‘yancin shigar da karar a kotun, yana mai cewa a gaban kotun sauraren korafe-korafen zabe ne kawai ya kamata a shigar da kasrr, a maimakon babbar kotun tarayyar da ke Abuja.
Tuni dai aka rantsar da Tinubu a matsayin sabon shugaban kasar Nijeriya a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.
A wani labarin na daban kotun Shari’ar Musulunci da ke Goron Dutse a Kano ta tura wani magidanci Auwalu Mai Yashi Kabara zuwa gidan yari.
Wani mai suna Alhaji Sabo Ado Kurawa ne ya yi kararsa a Kotun bisa zargin ya ci masa mutunci tare da barazana da rayuwarsa zargin da ya musanta.
Mai Yashi ya ce tun da farko Babban Malamin nan Sheikh Qariballah Nasiru Kabara ne ya yi ƙorafi a ofishin ƴan sanda na Mandawari bisa zargin Auwaulun ya ki ya daina sayar da yashi a kofar gidansu da suke yin Zikiri.
Daga nan ne jami’an ‘yansandan suka kama shi tare da tsare shi.
Auwalu Mai Yashi ya shaida wa Kotu cewa bai san Alhaji Sabo Kurawa ba sai a ofishin ‘yansanda na Mandawari, inda a nan ne ya zo a matsayin wakilin Khalifa Qariballahi.
Kuma har suka yi sa’insa da shi a ofishin ƴan sandan, amma ga mamaki an kai shi Kotu ba bisa zargin sayar da Yashi ba.
Yayin zaman Kotun na yau mai shari’a Malam Salisu Ƙoki ya umarci a kai Auwalu Mai Yashi zuwa Kurkuku har zuwa ranar 27 ga watan Yunin da muke ciki.