Yayin da Hukumar Zaben Nijeriya ke kokarin ganin al’ummar kasar wadanda ba su da katin zabe ko masu neman sauya akwatin zabe da sauransu sun yi rajista ta hanyar amfani da shafin Intanet, ga dukkan alamu yankin Arewa na samun koma-baya wajen yawan masu rajistar.
Akwai abubuwan dubawa game da al’ummar Arewa musamman yadda aka bar yankin a baya.
An sha yin guna-guni game da wannan sabon tsari na yi rajistar zaben ta intanet, tun a farkon fara wannan rajista da hukumar ta kaddamar ranar 28 ga Yunin wannan shekara, inda a mako guda kacal da farawa, alkaluma suka nuna kundanci ya bai wa arewaci tazara, wanda masana ke kallonsa a matsayin wata barazana ta daban ta fuskar siyasa ga Arewa.
Kamar yadda kididdigar masu rajistar ta Hukumar INEC ta nuna a mako na tara da fara rajistar, wadanda suka kammala rajistar sun kai mutum dubu dari biyar da sittin da tara da dari takwas da ashirin da takwas (569,828). Wadanda kuma suka gabatar da bukatar yi amma ba su kai ga kammalawa ba sun kai mutum miliyan biyu da dubu dari hudu da tamanin da biyar da dari bakwai da saba’in (2,485,770). Bayanin hukumar ya kuma nuna cewa, wadanda suka mika bukatar sauya akwatin zabe da masu neman a canza musu katin zaben sun kai mutum miliyan uku da dubu dari uku da ashirin da biyar da dari bakwai da arba’in da hudu (3,325,741).
Kididdigar ta fayyace adadin yawan masu neman rajistar a kowace shiyya daga cikin manyan shiyyoyin siyasa shida na fadin kasar nan har da Babban Birnin Tarayya Abuja, kamar haka:
Arewa Maso Yamma
Sakkwato: 37,012, Kebbi: 13,618, Zamfara: 38,638, Katsina: 17,478, Kano: 116,657, Jigawa: 24,897, Kaduna: 64,389.
Arewa Maso Gabas
Bauchi: 41,162, Yobe: 9,604, Gombe: 63,841, Borno: 8,798, Adamawa: 27,627, Taraba: 55,591
Arewa Ta Tsakiya
Kwara: 59,859, Neja: 43,214, Nasarawa: 30,895, Kogi: 84,297, Benue: 23,350, Babban Birnin Tarayya Abua: 91,726 da kuma Filato: 43,204.
Kudu Maso Yamma
Ogun: 39,245, Oyo: 56,498, Ekiti: 47, 266, Osun: 379,914, Ondo: 41,993, Legas: 88,309
Kudu Maso Kudu
Edo:209, 094, Delta:167,271, Bayelsa:199,148, Ribas: 65.905, Akwa Ibom: 56,518
Kuros Riba: 55, 415
Kudu Maso Gabas
Inugu: 10,373, Ebonyi: 14,750, Abiya: 12, 919, Imo: 27,095, Anambara: 118,200
Wannan kididdigar dai ta nuna cewa, Jihar Osun ke kan gaba a wadanda suka yi rajistar da mutum 379,914 yayin da Jihar Bayelsa ke biye da ita da mutum 199,148. Jihar Yobe ce ta karshe a yawan wadanda suka yi rajistar a fadin tarayya kasar nan da mutum 9,604 kacal.
Haka kuma a yankin arewacin kasar nan, kididiigar ta nuna cewa, Jihar Kano ce ke kan gaba da mutum dubu dari da shashida da dari shida da hamsin da bakwai (116,657), yayin da Jihar Yobe take ta karshe.
Idan aka dubi kididdigar wadanda suka gabatar da bukatar yin rajistar, za a ga jihohin kudu da wasu na arewa suka ninninka su a yawan jama’a, sun fi su adadin masu nema. Misali, Jihar Osun mai adadin mutum miliyan uku da dubu dari hudu da shashida da dari tara da hamsin da tara (3,416,959 a kidayar 2006), ta ninninka Jihar Kano mai yawan mutum miliyan tara da dubu dari hudu da daya da dari biyu da tamanin da takwas (9,401,288 a kidayar 2006). Watu Osun ta fi Kano da yawan masu rajista dubu dari biyu da sittin da uku da dari biyu da hamsin da bakwai (263,257 bisa jadawalin da ke saman a mako na tara).
Har ila yau, Jihar Bayelsa mai adadin mutum miliyan daya da dubu dari bakwai da hudu da dari biyar da shabiyar (1,704,515 bisa kidayar 2006) tana da adadin masu neman rajistar mutum dubu dari da casa’in da tara da dari da arba’in da takwas (199,148), inda ita kuma Jihar Kaduna mai adadin mutum miliyan shida da dubu dari da sha’uku da dari biyar da uku (6,113,503 a kidayar 2006) take da adadin masu neman rajistar mutum dubu sittin da hudu da dari uku da tamanin da tara (64,389). Idan aka duba, za a ga Jihar Bayelsa ta ninka Jihar Kaduna sau biyu har da kari, tun da ta fi ta da adadin masu neman rajista dubu dari da talatin da hudu da dari bakwai da hamsin da tara (134,759). Haka nan ta fi Jihar Kano da adadin masu rajista dubu tamanin da biyu da dari hudu da casa’in da daya (82,491).
Irin wannan lamari ne ya janyo Gamayyar Kungiyoyin Arewa ta CNG ta gudanar da taron manema labarai a Kaduna a kwanan baya domin nuna rashin gamsuwarta da tsarin rajistar.
Kungiyar ta bayyana fushinta akan lamarin wadda ta kira da “wani shirin yi wa yankin arewar zagon kasa”.
Masharhanta sun bayyana wa LEADERSHIP Hausa abubuwan da suke ganin su ne musabbabin samun koma-bayan yankin ta fuskar yin rajistar.
Wani babban lauya mai sharhin al’amuran yau da kullum, Barista Umar Mainasara Kogo, ya bayyana wa LEADERSHIP Hausa abubuwan da yake ganin su ne musabbabin koma-bayan da Arewa ke samu a rajistar.
“Arewa dai akwai dalilai da dama da ke kawo koma-baya wajen maganar rajistar katin dan kasa ko katin zabe. Idan mutum ya yi la’akari da abubuwan da suke tafiya su dawo, Arewa muna da karancin ilimi na sanin muhimmancin harkar zabe. Ba komai ya kawo karancin ilimi ba, ‘yan siyasa ba su damu da ilmantar da jama’a ba, kuma a Arewa ‘yan siyasa sun mayar da talakawa kamar Tawul ne, lokacin da su ke son goge zufa su goge in sun gama su wurgar da su.
“A Arewa har yanzu ba mu san romon dimokuradiyya ba, ba ma gani a kasa, wadanda ake zaba sun mayar da talaka kamar tsani ne da sun riga sun haye samansa sai su jeho da tsanin ya fado kasa, kuma maganar gaskiya ita ce, a Dimokuradiyyar nan Arewa ita ta fi koma-baya, mun zama shalkwatar talauci, kamfanoni da kuma gurabe wadanda suke na aikin da matasa za su samu ayyuka duk sun mutu, babu inda ake da ma’aikar takin zamani da talaka manomi zai iya cewa eh ga alama nan ta lasar romon dimokradiyya,” in ji shi.
Ya ci gaba dacewa, “da yawa kasuwanninmu sun rufe, babu harkar kasuwanci, talakawammu an rufe kan iyaka ba sa iya shigo da abubuwa ko su fitar da su, harkar rashin tsaro ta tarwatsa mutanemmu ta razana su, mutanemmu sun girgiza ba su san inda suke ba, suna fama ne da yaya za su samu inda za su samu nutsuwa ta harkar tsaro zuciyarsu ta yi dai-dai da ruhin jikinsu, ba wai magana ake ta tunanin zabe ba, a yayin da suke ganin wadanda suka zaba sun juya musu baya sun wulakanta su, ba su tunanin yi wa jama’a wani abu ballantana a ce za a cika alkawura, to gaskiyar magana wadannan su ne abubuwan da suka tattaru suka sanya talakawa suka juya baya.
“Daidai ne wadanda za ka ga suna da alaka da wadansu su ne za ka ga suna zuwa suna yin zabe. A gaskiya sai an tashi an yi hobbasa, sai ‘yan siyasa sun tashi canza akidarsu da manufofinsu da tunaninsu, sannan talaka zai tsaya ya bata lokacinsa ya rika yin hidimomi saboda harkokin siyasa.
“‘Yan siyasa hakika sun kasa wajen sauke nauyi da alkawura da suka daukarwa talakawan Arewa, kuma wannan shi ya sanya ka ga talakawan Arewa ba su ba da muhimmanci ba wajen sabunta rajistar da ake yi.
“An fi yi wa mutanen kudu ayyuka, kuma an fi biya wa ‘yan Kudu bukatunsu fiye da na ‘yan Arewa, don haka wannan gaskiyar magana kenan wacce take da daci, shi ya sa ka ga da yawan mutanemmu gaba daya abin bai dame su sosai ba, saboda an mayar da su kawai ‘yan turin mota, in ta tashi ta watsa musu kura ko ta watsa musu tabo ta yi gaba, wadanda ke cikin motar suna jin dadinsu daban, wadanda kuma aka bari daban shi kenan.
“Da yawa za su zo suna ta fafutuka a zabe su, wasu ma da an zabe su, irin motocin ma da su ke shiga da irin gilashin da suke sawa mai shuni babu yadda za a yi ka gane su ballantana ma talaka ya ce zai iya kawo korafi. To wannan sai ‘yan siyasa sun tashi tsaye sun yi la’akari da cewa akwai matsala sun kuma yi gyara sannan mutanenmu za su hankalta sosai a kan siyasar 2023 da ke tafe.” Kamar yadda ya bayyana.