Kotun koli ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf na jami’yyar NNPP a matsayin halastaccen Gwamnan Jihar Kano.
Kotun koli ta warware hukuncin da kotun sauraron kararrakim zabe da kotun daukaka kara suka zartar a baya.
Kwamitin alkalai guda biyar sun ce hukuncin da kotun kasa ta yi na soke kuri’u 165,616 Gwamna Yusuf na daidai ba ne.
Hukuncin da mai shari’a Inyang Okoro ya yanke ya kuma ce batun zama dan jam’iyya na Gwamna Yusuf wannan hurumin jam’iyya ne.
Ya ce binciken da suka yi karkashin sashe na 177 (c) na kundin tsarin mulkin Nijeriya da sashe na 134 (1) na dokar zabe, babu hujja da ta nuna Gwamna Yusuf ba dan jam’iy
yar NNPP ba ne.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, sun isa kotun kolin Nijeriya a yau Juma’a domin sauraren hukuncin karshe kan zaben gwamnan jihar da aka yi a ranar 18 ga watan Maris.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa za a raba gardama tsakanin Gwamna Yusuf na jam’iyyar NNPP da babban abokin hamayyarsa a zaben, Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC.
Kotun koli ta tsayar da ranar Juma’a 12 ga watan Junairu, 2024 domin yanke hukunci kan karar da gwamna Yusuf ya shigar kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a baya, na tsige shi daga kujerar gwamnan jihar.

LEADERSHIP ta hangi wasu gwamnonin jihohin da su ma za a yanke hukunci kan shari’ar zaben jihohinsu.
Source: LEADERSHIPHAUSA