Karamin ministan kwadugo da samar da ayyukan yi, Festus Keyamo, ya fadi babban makamin da Tinubu zai amfani da shi Keyamo, kakakin kwamitin yakin neman zaben APC ya ce Peter Obi ya gama yi wa Tinubu aiki.
A cewarsa, daukakar da Peter Obi ya samu a takarar da ya fito zata saukaka wa APC ta sake lashe zabe cikin sauki.
Mai magana da yawun kwamitin kamfen shugaban kasa na APC, Festus Keyamo ya bayyana babban tanadin da jam’iyyar ke da shi na ci gaba ba mulki a zaben 2023.
Jaridar The Cable ta rahoto cewa Keyamo ya bayyana Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a inuwar LP da “Babban makami” wanda APC zata yi amfani da shi ta ci zaben 2023.
Mista Keyamo, karamin ministan kwadugo da samar da ayyukan yi, ya yi wannan furucin ne yayin da yake hira da kafar Talabijin din ARISE ranar Laraba.
Yace tafiyar Obi ta maida zaben 2023 dake tafe ya koma tseren mutum daya wanda ya yi wa APC alfarma.
Ministan ya kara da cewa dan takarar shugaban kasa na LP ya ja rabonsa a cikin magoya bayan PDP sun koma tafiyarsa, ya haddasa wa babbar jam’iyyar adawa matsala.
“Zancen gaskiya shi ne wannan zaben mai zuwa an gama shi tuntuni, tsere ne na gwarzo daya, ba ina zuzuta dan takararmu bane saboda ina matsayin kakaki amma duk mai sa ido a hankalce ya san sakamako ba zai ba da mamaki ba.”
“Rigingimu sun kewaye PDP ta ko ina ciki da waje, duk wanda ya goyi bayan PDP a 2019 ya kama gabansa.
Ohaneze Ndigbo, Middle Belt Forum, PANDEF, Afenifere, Obasanjo da Ayo Adebanjo duk Atiku suka goyi baya a 2019.”
“Amma yanzun sun raba gari da shi sun koma bayan Labour Party. Mun fada cewa Obi ne babban makamin da Asiwaju ke da shi.
Obi ne babban dalilin da zai ba Bola Tinubu nasara a zaben nan.” – Festus Keyamo.
Har yanzun muna sa ran PDP ta dunkule – Diri da Obaseki
A wani labarin kuma Gwamnonin PDP Biyu Sun Ziyarci Okowa, Sun Nanata Bukatar Hada Kai da gwamnonin G5.
Gwamnan Bayelsa da takwaransa na jihar Edo sun ziyarci gwamna Okowa a jihar Delta, sun masa fatan zama mataimakin shugaban kasa.
Duoye Diri da Godwin Obaseki sun ce har yanzun suna fatan shawo kan tawagar G5 da Wike ke jagoranta don a dunkule wuri daya.