Tsohon jagoran ‘yan hamayya na Kenya Raila Odinga ya kaddamar da yakin neman zabensa karo na biyar na shugabancin kasar, wannan karon tare da goyon bayan tsohon abokin hamayyarsa, Shugaba Uhuru Kenyatta.
An samu mummunan rikici bayan zaben musamman 2007, kuma daman kusan a duk zabukan da aka rika yi na baya Mista Odinga yana zargin an yi masa murdiya.
Yanzu dai Shugaba Kenyatta ba zai samu damar sake tsayawa takara a zaben shekara mai zuwa ba 2022, bayan wa’adi biyu da ya yi.
A gaban dubban magoya baya ne a babban filin wasa na babban birnin kasar, Nairobi, Raila Odinga mai shekara 76 ya rika jinjina tare da yaba wa Shugaba Uhuru Kenyatta bisa abin da ya ce hangen nesansa na bullo da batun tattaunawa domin sasantawa da kuma hada kan abokan hamayya ko gabar biyu a da.
Sabani ne da rikici da ya dade yana wakana tsakanin ‘yan gidan siyasar biyu, domin abu ne da suka gada a tsakaninsu, kasancewar, mahaifin shugaban kasar na yanzu Uhuru Kenyatta wato Jomo Kenyatta lokacin da yake kan mulki a 1969 ya daure mahaifin shi Raila Odinga, wato Jaramogi Oginga Odinga, wanda shi ne jagoran ‘yan hamayya a lokacin.
Iyalan gidajen biyu dai sun kankane siyasar kasar tun bayan da ta samu mulkin kai daga Birtaniya a 1963, inda a lokacin Jomo Kenyatta ya kayar da Odinga a zaben farko na kasar ta gabashin Afirka.
Wannan sasantawa ta yanzu tsakanin jagororin biyu kusan abu ne da ake kallo a matsayin wani yunkuri na hana mataimakin shugaban kasar na yanzu William Ruto, gadon kujerar shugabancin kasar bayan Uhuru Kenyatta ya sauka.