Kotu ta tabbatar da zaben gwamna Nasir Idris a matsayin zababben gwamnan jihar Kebbi.
Kotun sauraren kararrakin zabe ta jihar ta Kebbi, karkashin jagorancin mai shari’a Ofem I. Ofem ta yanke hukuncin ne a ranar Alhamis.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana Idris na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kebbi da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Amma, Janar Aminu Bande (mai ritaya) na jam’iyyar PDP ya shigar da kara inda ya kalubalanci zaben gwamna Idris a zaben da aka yi ranar 18 ga watan Maris.
A wani labarin na daban a jiya Alhamis ne Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya karɓi baƙuncin matar nan da ‘yan bindiga suka raba da muhallinta da aka yaɗa a wani faifan bidiyo.
Faiaifan bidiyon ya nuna wata uwa da ‘ya’yanta tana bayani a kan ‘yan bindiga suka tilasta musu cin ciyawa domin su tsira da rayukansu.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar ta Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce halin da matar wacce ta rasa matsugunin ke ciki ya nuna cewa akwai bukatar a ɗauki matakin gaggawa don magance musabbabin Ibtila’in da yake raba mutane da muhallansu same su da kuma samar matakawuna da kuma tabbatar da cewa iyalai suna samun abubuwan bukata na rayuwa.
Ta ƙara da cewa Gwamnan ya karɓi baƙuncin matar da ta rasa muhallin nata ne a matsayin nuni kan jajircewarsa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Zamfara.
gwamna
“A yau (Alhamis) ne Gwamna Dauda Lawal ya karbi baƙuncin Hauwa’u Halliru, wadda ta rasa komi a dalilin tu’annatin ‘yan fashin daji.
“Gwamna Lawal ya bayyana ƙudirinsa na kawo ƙarshen rashin tsaro a jihar tare da jajanta wa iyalan da ɓarnar ‘yan fashin dajin ta shafa.
“A matsayinsa na shugaba mai tausayi, Gwamna Lawal ya gaggauta samar wa matar da ta rasa muhallin nata gida mai kyau da aka sa wa komai na more rayuwa.
“Ya kuma tabbatar mata da kudirin gwamnatinsa na ciyar da iyalinta abinci da sauran abubuwan bukatu, ta yadda za ta sake gina rayuwarta cikin mutunci da tsaro.
“Bugu da kari, gwamnan ya umarci kwamishinan ilimi, kimiya da fasaha da ya tabbatar da shigar da ‘ya’yanta makaranta cikin gaggawa da kuma samun cikakken tallafin karatu.
“Ya kuma bukaci dukkan hukumomin da abin ya shafa da su ƙara ƙaimi wajen zakulo iyalai marasa galihu da ke fuskantar irin wannan ƙalubale tare da ba su tallafin da ya dace.
“A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar Masu Kare Hakkin Bil’adama, Kwamared Salisu Umar, ya bayyana matukar jin daɗinsa kan yadda Gwamnan Jihar Zamfara ke ƙoƙarin tabbatar da tsaro da jin daɗin jama’a.
“Ya kuma yaba da yadda gwamnan ya nuna himma, tare da bayyana cewa wannan ne karon farko da ya ga irin wannan kyakkyawar shugabanci a jihar, inda ya ƙara da cewa kalaman nasa sun yi daidai da ra’ayoyin jama’a, wadanda suka dade suna jiran shugaban da zai riƙa sanya buƙatunsu a gaba.” In ji sanarwar.
Source LEADERSHIPHAUSA