Gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya bukaci jam’iyyun adawa da su hada kai da gwamnatinsa domin gina kyakkyawan shugabanci da bunkasa tattalin arzikin jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a fadar gwamnati da ke Birnin Kebbi a sakonsa na fatan alheri ga al’ummar jihar bayan halartar Sallar Eid-el-Fitr a babban masallacin Sallar Idi a Birnin Kebbi.
“Yanzu da aka kammala zabe da siyasa, ina gayyatar al’ummar jihar na kowane bangare ba tare da la’akari na jam’iyya ba. Mu hada kai na gani ci gaban jihar mu domin kaiwa ga matakin ci gaban da ake so”.
“Mafi yawan jama’a sun zabe ni, ina gode musu da sauran su bisa goyon bayan da suka ba ni, da aminci da kuma hadin kai,” inji shi.
Ya tabbatar da cewa gwamnati za ta tabbatar da samar da ababen more rayuwa, tattalin arziki, noma, bunkasa ilimi da samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga al’umma.
“Babban asibitocin da ke Argungu, Yauri da Zuru, za a gyara su tare da samar da kayan aiki na zamani don yi wa mazauna yankin hidima da kuma gudanar da ayyukansu a matsayin cibiyoyin kiwon lafiya ba tare da sun kawo masara lafiya a babban birnin Jihar ba” in ji shi.
Ya taya al’ummar jihar Kebbi murnar kammala azumin watan Ramadan da kuma murnar bukukuwan karamar Sallah.
Shima a nasa bangaren gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf Kabir ya bukaci mazauna jihar da su rungumi halayen tausayi, karamci, da’a, kishin kasa, da zaman lafiya domin ci gaban jihar da kasa baki daya.
A cewar Gwamnan a sakonsa na Sallah a Kano ranar Laraba, ya kamata kowa ya ci gaba da koyi da irin wadannan kyawawan halaye har gaban watan Ramadan.
A yayin da yake taya daukacin al’ummar jihar da Shugaba Bola Tinubu da daukacin al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan, Gwamnan ya sake nanata aniyarsa ta cika alkawuran da ya dauka yayin yakin neman zabensa.
DUBA NAN: Hukumar Kashe Gobara A Kano Ta Ceto Dukiyar Miliyan 130
Gwamna Abba Yusuf ya bayyana kwarin gwiwar cewa, ‘bayan wuya sai daɗi’, inda yace, gwamnatinsa ta shirya aiwatar da manyan ayyukan raya kasa a shekarar 2024.