Akalla Kasashen Turai 20 suka bayyana goyan bayan su ga shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Gebreyesus domin ci gaba da rike kujerar sa zagaye na biyu, a daidai lokacin da gabatar da takarar shugabancin hukumar ya cika a wannan alhamis din.
A sanarwar da suka gabatarwa manema labarai a Majalisar Dinkin Duniya, Kasashen Jamus da Faransa sun ce duk sun goyi bayan sake takarar Gebreyesus domin cigaba da gudanar da aikin da yake a hukumar.
Daga cikin kasashen suka bayyana goyan bayan shugaban hukumar akwai Austria da Faransa da Jamus da Portugal da kuma Spain, yayin da a ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa ake saran bude sunayen kafin gabatar da su ga wakilan kasashe 194 dake Majalisar Dinkin Duniya domin amincewa.
Kasashen duniya da dama sun yaba da jagorancin Gebreyesus musamman lokacin da aka samun barkewar annobar korona, yayin da ya fuskanci matsin lamba daga shugaban Amurka na wancan lokaci Donald Trump wanda ya janye kasar daga cikin hukumar.
Trump ya zargi shugaban hukumar da goyawa China baya wajen boye gaskiyar abinda yayi sanadiyar haifar da annobar korona.
Ya zuwa wannan lokaci babu wani ‘dan takarar da ya gabatar da takardun sa domin fafatawa da shugaban Hukumar.