Gwamnatin rikon kwaryar kasar Libya na karbar bakunci wakilan kasashen duniya da ke halartar wani taro kan yadda za a samar da hadin kai tsakanin ‘yan kasar gabanin babban zaben da ake shirin gudanarwa a cikin watan disamba mai zuwa.
Wasu daga cikin kasashen Duniya sun soma nuna goyan baya ga tsarin sake dawowwa da mulkin farrar fula kusan shekaru goma da mutuwar Ghadafi a kasar ta Libya.
A watan yuni shekarar bana ne Faransa ta sake bude ofishin jakadancinta da ke birnin Tripoli na kasar Libya, bayan da aka rufe shi shekaru 7 da suka gabata saboda tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan boren da aka yi wa gwamnatin Kanar Kaddafi.
A wani labarin na daban kuma mai kama da wannan gwamnatin Libiya ta bude babbar hanyar da ta sada yankunan gabashi da kuma yammacin kasar da suka jima a rabe, sakamakon yakin basasar da ya biyo bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Mu’ammar Gaddafi a shekarar 2011.
Fira Ministan Libya Abdul Hamid Dbeibah ya jagoranci kawar da guma-guman duwatsu da kuma tarin kasar da aka yi amfani da su wajen raba yankunan na Yammaci da Gabashin Libya.
An dai shafe tsawon lokaci ana fafatawa tsakanin Sojojin Gwamnatin Libya da mayakan Janar Khalifa Haftar da ke iko da yankin gabashin kasar, kafin daga bisani a cimma yarjejeniyar sulhun da ta kai ga kafa sabuwar gwamnati a karkashin Fira Ministan Abdul Hamid.