Kwararru kan tattalin arziki na kasa da kasa, sun yi gargadin cewa yawan kudaden da kasashe masu tasowa ke kashewa wajen biyan bashin da ake binsu yayi hauhawar da ba a taba ganin irinta ba cikin fiye da da shekaru 20 da suka gabata.
Matsalar tattalin arzikin kasashe masu tasowa kuma ta yi kamari ne, a yayin da kuma shirin rangwame na dakatar da biyan bashin da suke yi wanda ke karkashin kasashe masu hannu da shuni ke shirin karewa.
A farkon wannan watan Bankin Duniya ya ce tasirin annobar Korona ya bar kusan kashi 60% na kasashe masu karamin karfi a cikin hatsarin bashi.
Rahoton Cibiyar nemawa kasashe masu tasowa ‘yanci daga bautar biyan basuka na rashin adalci ya nuna cewa biyan bashin kasashe masu tasowa ya karu da kashi 120 cikin 100 tsakanin shekarar 2010 zuwa 2021, wanda ya kai matakin da ya fi girma tun daga shekarar 2001.
A duniya baki daya, kasashe 54 a halin yanzu ke cikin rikicin basussuka.
A wani labarin na daban Bankin Duniya ya bayyana Najeriya a matsayin kasa ta biyar da ta fi karbar bashi daga gare shi, bayan da gwamnatin kasar ta ciwo bashin dala biliyan 11 da miliyan 700, kwatankwacin kimanin naira tiriliyan 4 da biliyan 816.
Rahoton Bankin Duniyar ya bayyana India a matsayin kasar da ke kan gaba a tsakanin masu karbar bashin, inda a yanzu haka nauyin da ke kanta ya kai dala biliyan 22, sai Bangladesh a matsayi na biyu bayan karbar jumillar bashin dala biliyan 18, yayin da Pakistan ke da nauyin bashin dala biliyan 16 da kusan rabi.
Sauran kasashen dake matakai biyar na farko sun hada da Vietnam mai dauke da nauyin bashin dala biliyan 14, sai kuma Najeriya mai bashin dala biliyan 11 da miliyan 700.
Dalar Amurkan biliyan 11 da miliyan 700 kwatankwacin naira tiriliyan 4 da biliyan 816 da ke Najeriya, kusan kashi daya bisa uku na kasafin kudin kasar ne na shekarar 2021 wanda ya kai Naira tiriliyan 13 da biliyan.
Kasashen Afirka da ke bin bayan Najeriya wajen nauyin bashin Bankin Duniyar da ke kansu sun hada da Habasha mai dala biliyan 11 da miliyan 200, Kenya mai dala biliyan 10 da miliyan 200, sai Tanzania mai dala biliyan 8 da miliyan 300.
Kasa ta 9 wajen nauyin bashin a Afirka ita ce Ghana mai dala biliyan 5 da miliyan 600, sai Uganda da ke da bashin dala biliyan 4 da miliyan 400.