Kungiyoyin kwallon kafa daga kasashe duniya daban daban na fafata wasanin neman gurbi a gasar cikin kofin duniya da kasar Qatar zata karbi bakwanci a shekarar 2022. Ya zuwa yanzu kasashe takwas suka samu tikitin shiga gasar mai farin jinni na badi, amma ya zuwa yanzu babu kasar Afirka ko guda da ta karbi tikiti biyar da aka tanada musu.
Kasashe da suka karbi tikiti
Tuni dai kasashen Jamus da Denmark da kuma Brazil suka samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA karo na farko da zai gudana a yankin Gabas ta Tsakiya.
Sauran kasashe sun hada da Faransa da Belgium da suka sami damar shiga gasar a ranar Asabar bayan da suka doke Kazakhstan da Estonia. Faransa ta doke Kazakhstan da ci 8-0, yayin da Belgium ta doke Estonia da ci 3-1.
Dan wasan gaba na Faransa Kylian Mbappe shi kadai ya jefawa kwallaye 4 daga cikin 8 da kasar sa ta jefa a wasan da akayi, yayin da Karem Benzema ya jefa 2, sai kuma Rabiot da Antoine Griezmann da suka jefa kwllo guda-guda.
A wasan baya-bayan nan Crotia da Spain da Serbia sun samu nasu tikin zuwa gasar.
Babu kasar Afirka da ta haye
Ya zuwa yanzu babu kasar Afirka da ta samu tikin shiga gasar ta neman cin kofin duniya da Qatar zata karbi bakwanci, kuma kasashe biyar ne zasu wakilci nahiyar.
Sai dai jamhuriyar Congo da Masar da Ghana da Mali da Morocco da kuma Senegal sun kai zagayen karshe na fafatawar samun gurbi.
Sai kuma kasashen dake daf da zuwa zagen karshe na wasannin neman gurbi da suka hada da Algeria da Burkina Faso da Cafe Verde da Kamaru da jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sauran kasashen sun hada da Cote d’Ivoire da Equatoril Guinea da Nigeria da Tunisia da kuma Zambia.
Za’a kammala wasannin a watan Yunin 2022
An fara wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA 2022 a watan Yunin shekarar 2019 kuma ana sa ran kammalawa a watan Yunin 2022.