Amurka, da Canada da Australia sun shiga jerin kasashe da suka dakatar da zirga-zirga tsakaninsu da Afirka ta Kudu a ranar Asabar, bayan gano sabon nau’in cutar Korona na Omicron a kasar, wanda a yanzu haka ya firgita hukumomin kasa da kasa.
Kawo yanzu tuni Biritaniya, Jamus da Italiya da kuma Jamhuriyar Czech suka tabbatar da bullar sabon nau’in cutar Koronar na Omicron a cikinsu.
A baya bayan nan Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadin cewa sabon nau’in cutar na Korona na iya yaduwa cikin sauri fiye da sauran nau’ikan annobar.
A bangaren kwararru kuwa, sun yi gargadin cewa mai yiwuwa hukumomi sun lattin daukar matakin hana tafiye-tafiye don dakile yaduwar sabon nau’in Koronar na Omicron zuwa sassan duniya.
A wani labarin na daban ma’aikatar lafiyar Afirka ta Kudu ta caccaki kasashen da suka haramta zirga-zirga tsakaninsu da kasar don dakile yaduwar sabon nau’in cutar Korona, matakin da Afirka ta Kudun ta bayyana a matsayin mugunta, da rashin kwarewa a fannin kimiyya, wanda kuma ya sabawa shawarar hukumar lafiya ta duniya WHO
Yanzu haka dai bayanai sun tabbatar da cewar, sabon nau’in Koronar mai suna Omicron da ya bulla daga Afirka ta Kudu, ya bazu zuwa Hong Kong, Belgium, Isra’ila da kuma Botswana.
Biritaniya ce dai kasa ta farko da ta dauki matakin haramta zirga-zirga tsakaninta da kasashen kudancin Afirka, sa’o’i kadan bayan da Afirka ta Kudu ta bayyana gano sabon nau’in Koronar na Omicron da ke iya rikidewa zuwa wasu karin sabbin nau’ikan.
Daga bisani ne kuma kasashen Austria, Canada, Faransa, da Jamus, da Italiya, da Netherlands da kuma Amurka suka bi sahun Birtaniyar wajen dakatar da zirga-zirgar jiragen sama daga yankin kudancin nahiyar Afirka, musamman ma daga Afirka ta Kudun.
Sai dai kuma a ranar Juma’a hukumar lafiya ta Duniya WHO ta yi kira ga kasashe da su guji daukar matakin na haramta zirga zirga da wata kasa ko yanki a wannan mataki da ake ciki.
A halin da ake ciki dai, cin-cirindon matafiya sun kasance tsaye kan dogayen layuka a filin jiragen sama na kasa da kasa dake birnin Johannesburg tun a ranar Juma’a da zummar hawa jiragen da za su yi balaguron karshen ficewa daga Afirka ta Kudu, biyo bayan matakin haramta zirga-zirgar da kasashe da dama suka dauka tsakaninsu da kasar, bayan gano sabon nau’in cutar Korona na Omicron.
Akasarin matafiyan dai sun yanke hutu ko kuma yawon bude idon da suke yi a Afirka ta Kudun ne, gudun kada haramcin tafiye-tafiye tsakanin baki daga kasar zuwa yankunansu ya rutsa da su na tsawon lokaci.