Dan wasan gaba na Tottenham Harry Kane ya bayyana gamsuwa da salon kamun ludayin sabon manajan kungiyar Antonio Conte da ya maye gurbin Nuno Espirito Santo, bayan kai kungiyar ga nasara a wasan farko da ya jagorance ta.
A daren jiya Alhamis ne dai Tottenham ta yi nasarar lallasa Vitesse Arnhem da kwallaye 3 da 2 karkashin gasar Europa wanda ya bai wa magoya bayanta kwarin gwiwar yiwuwar Conte ya samar da sauyi a kungiyar mai fama da mashasshara.
Duk da cewa kwallo guda tal Kane ya iya zurawa a wasanni 9 da ya doka cikin wannan kaka, Kaftin din na Ingila ya ce da yiwuwar Tottenham ta murmure daga koma bayan da ta ke fuskanta karkashin jagorancin Conte wanda ya horar da kungiyoyin kwallon kafa na Juventus da Chelsea da kuma Inter Milan.
Shi kansa Antonio Conte yayin zantawarsa da manema labarai, ya ce ya na da kwarin gwiwar samar da gagarumin sauyi a kungiyar mai doka firimiya nan da dan wani lokaci, kamar yadda kane ya kyautata masa zato.
Tottenham dai ta raba gari da Nuno wanda tsohon manajan Wolves ne watanni 4 bayan bashi ragamar kungiyar wadda rabonta da abin kirki tun bayan tafiyar Mauricio Pochettino wanda ya iya kaita har wasan karshe na cin kofin zakarun Turai a 2019.
A wani labarin na daban hukumar Lafiya ta duniya WHO ta sahale fara amfani da nau’in rigakafin corona na Covaxin da kamfanin Bharat Biotech na India ya samar bayan gwajinsa tare da gano tasirinsa a yaki da cutar wadda zuwa yanzu ta hallaka mutane fiye da miliyan 5 a sassan Duniya.
Nau’in rigakafin na Covaxin shi ne irinsa na farko da aka samar tare da yin gwajinsa cikin kasar India kuma WHO ta sahale amfani da shi inbanda sauran rigakafi da kamfanonin magani na kasar ke taya aikin samar da su.
Acewar hukumar ta WHO nau’in rigakafin na da sahihancin kashi 78 wajen yaki da cutar ta covid-19 bayan gwajin allurarsa sau bibbiyu kan jama’a cikin makwanni 4 da suka gabata.
WHO ta bayyana cewa nau’in rigakafin na Covaxin zai yi tasiri hatta a kanana da matsakaitan kasashe la’akari da saukinsa wajen adanawa da kuma dadewar da ya ke gabanin lalacewa.
Nau’in rigakafin na India ya zama rigakafi na 8 da zuwa yanzu Duniya ke amfani da shi don yakar cutar bayan Pfizer da BioNTech da Moderna da AstraZeneca da Johnson and Johnson baya ga Sinopharm da Sinovac.