Daruruwan kanawa ne suka yi dafifi a yammacin ranar Litinin, don tarbar Gwamna Abba Kabir Yusuf da kotun daukaka kara ta kora, inda suka nuna alhininsu tare da yi masa addu’ar samun nasara a kotun koli.
Jama’a jihar sun mamaye titunan birnin Kano, inda suka yi ta fito daga shagunansu da gidajensu domin nuna goyon bayansu ga gwamnan da ya kai ziyara domin gudanar da ayyuka a cikin birnin.
Yusuf, ya bayyana ne bayan da kotun daukaka kara da ke Abuja ta kore shi, magoya bayansa ne suka tarbe shi daga gidan gwamnati zuwa Asibitin kwararru na Murtala da ke cikin garin Kano a yammacin ranar Litinin.
Jama’a kanawa sun mamaye tituna suna rera wakoki da jinjina tare da yi masa addu’a.
Leadership ts ruwaito cewa kotun daukaka kara da ke Abuja a ranar 17 ga watan Nuwamba, ta sake tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe da ta kori Gwamna Yusuf tare da bayyana Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin zababben gwamnan jihar.
Jama’ar da suka fito domin tarbar sa suna ta rera wakokin “Kano sai Abba, hudu sau hudu” (Kano ta Abba ce).
Gwamna Yusuf ya kaddamar da sashen bada agajin gaggawa na asibitin kwararru na Murtala Mohammed, daya daga cikin ayyuka da dama da ya fara tun bayan da aka zabe shi.
Kazalika, ya duba a jihar a yammacin na ranar Litinin.
Source: IQNAHAUSA