Gwamnan Borno Babagana Zulum, ya ce kananan hukumomi biyu da suka hada da Abadam da kuma Guzamala sun koma karkashin ikon mayakan ISWAP, tsagin da ya balle daga kungiyar ‘yan Boko Haram.
Yayin da yake yabawa gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da hukumomin tsaro bisa nasarorin da aka samu a Borno, Zulum ya ce ya damu matuka game da karuwar mayakan ISWAP a sassan Kananan hukumomin jihar, musamman daga bangaren kudanci, inda ya kara da gargadin cewa bangaren na ISWAP sun fi na Boko Haram karfi da kuma makamai.
Gwamnan ya koka kan cewar idan ba a gaggauta daukar mataki ba, barzanar na iya zama illa ba ga mutanen arewa maso gabashin Najeriya kadai ba, har ma da kasa baki daya.
Farfesa Babagana Zulum ya ce a watannin baya bayan nan Kananan hukumomin jiharsa sun samu kwanciyar hankali musamman a fannin noma sakamakon mika wuya da ‘yan tada kayar baya da dama suka yi ga sojoji.
A cewarsa, tun bayan da mayakan suka mika wuya, an samu karuwar noma gonaki da akalla kashi 700 cikin 100.