‘Dan takaran shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya kama hanyar Abuja da nufin ya fara kamfe.
Alhaji Atiku Abubakar da Gwamnonin jam’iyyar PDP za su kaddamar da kwamitin yakin neman zabe Jam’iyyun LP da APC sun dakatar da fara yakin zaben shugaban kasa, ba a san yaushe za su soma ba.
A ranar Laraba, 28 ga watan Satumban 2022 za a kaddamar da kwamitin kamfe na shugaban kasa na jam’iyyar PDP mai adawa.
Punch tace ‘dan takaran PDP a 2023, Atiku Abubakar ya isa garin Abuja tare da wasu gwamnonin jihohi da nufin a shiga kamfe da aka fara daga yau.
Ana sa rai Atiku Abubakar da ‘yan kwamitin yakin neman takaran za su hallara a babban dakin taro na ICC a garin Abuja domin bikin rantsarwar.
Ya za ayi da Wike a PDP?
Jam’iyyar PDP za ta fara aikin neman zabe ba tare da Gwamna Nyesom Wike da mutanensa ba.
Dr. Bukola Saraki yana ta kokarin shawo kansu.
‘Yan bangaren PDP da ke tare da Wike wajen yakar takarar Atiku sun hada da tsofaffi da gwamnoni masu-ci da tsofaffin ‘yan majalisa da Ministoci.
Ina Tinubu suka shiga?
A lokacin da Atiku yake shirin kaddamar da kwamtin neman zabe, ‘dan takaran jam’iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu ya tafi kasar waje.
Rahoton ya nuna shi ma Peter Obi mai neman mulkin Najeriya a zaben 2023 a karkashin LP ba zai fara yakin neman zaben shugaban kasa a yau ba.
Majiyarmu ta shaida mana cewa a makon nan ake sa rai ‘dan takaran NNPP, Rabiu Kwankwaso zai ziyarci jihar Filato domin bude ofishin jam’iyyarsu.
Har yanzu Sanata Rabiu Kwankwaso bai fito da manufofinsa ba, kuma ba a ji labarin ya kaddamar da ‘yan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa ba.
Dattawan Arewa za su tsaida ‘dan takara Kun ji labari Northern Elders Forum ta Dattawan Arewa tace kafin ta yanke shawara tsakanin ‘yan takaran na 2023, sai ta zauna da kowanensu tukuna.
Dr. Hakeem Baba-Ahmed yace an gama yin irin kuskuren da aka yi a baya, duk aka taru aka ce ‘Sai Baba’ a zaben 2015, a karshe bai yi masu rana ba.
Source:legithausang