Kwanaki kadan ya rage a gudanar da zaben gwamna a jihohin Kogi, Imo da Bayelsa, sai dai akwai wasu kalubalen da zabukan ka iya fuskanta, musamman na rashin tsaro da kaurace wa zaben da kuma yadda hukumar zabe mai zaman kanta za ta iya gudanar da sahihin zabe a daukacin jihohin ba tare da wata matsala ba.
Shi ya sa ma, tsohon shugaban kasa, Abdulsalami Abubakar da, Rabaran Mathew Hassan Kukah, sun yi kira ga daukacin ‘yan takara da magoya baya da su yi kokarin wajen gudanar da zabukan ba tare da tashe-tashen hankula ba.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da manyan ‘yan takarar gwamna a jihohin suke cacar baki tare da sukar juna, wanda hakan na iya haddasa tashe-tashen hankula a jihohinsu.
A yayin da zaben gwamna a jihohin uku zai gudana a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023, kwamitin zaman lafiya na kasa karkashin jagorancin Abdulsalami da Kukah ya damu matuka kan zaman lafiya da tsaro a jihohin, kuma ya bukaci ‘yan takarar su rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.
Akwai fargaba dangane kan dalilin da suka sa ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a lokacin zabe a Nijeriya duk da kokarin da hukumoma da sauran masu ruwa da tsaki ke yi.
A saboda haka, kwamitin zaman lafiya na kasa ya ce ba zai karaya ba har sai halayen wasu ‘yan siyasa sun sauya a lokacin zabe, inda ya dage cewa zai yi kokarin ganin an gudanar da zaben cikin zaman lafiya bisa jajircewar ‘yan takarar gwamna da jam’iyyunsu da sauran masu ruwa da tsaki.
A Jihar Imo
Da yake tofa albarkacin bakinsa, dan takarar gwamnan Jihar Imo a karkashin jam’iyyar PDP, Sanata Samuel Anyanwu, ya ce matakin da gwamnatin jihar take dauka na tunkarar kalubalen tsaro ne ke haddasa tashe-tashen hankula a jihar.
Anyanwu ya ce matasan jihar ba su da aikin yi, inda ya shawarci gwamnati da ta samar da ayyukan yi da gina masana’antu da samar da yanayin da zai taimaka wajen bunkasa kasuwanci.
A cewarsa, hakkin gwamnati ne ta kare rayuka da dukiyoyin al’umma, ya idan gwamnati ta kasa haka, za a kira ta da sunan wacce ta gaza.
A nasa bangaren, dan takarar gwamna na jam’iyyar LP, Sanata Athan Achonu ya kuma zargi gwamnatin jihar kan rashin tsaro a jihar.
‘Yan takarar sun nuna cewa a shirye suke su rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da kuma kudurin gudanar da zabe ba tare da tashin hankali ba.
Sai dai kuma, gwamnan jihar kuma dan takara a karkashin jam’iyyar APC, Hope Uzodimma y ace gwamnatinsa tana kokari wajen magance duk wani kalubalen da ka iya shafar zaben.
Kwamishiniyar zaben jihar, Farfesa Sylbia Agu ta bayyana cewa hukumar zaben ta yi isassun shirye-shirye tare da jami’an tsaro wajen kare ma’aikatanta.
A Jihar Kogi
A Jihar Kogi, dan takarar gwamna na jam’iyyar SDP, Murtala Ajaka, ya nuna sha’awarsa na sanya hannu kan duk wata yarjejeniyar zaman lafiya.
LEADERSHIP tuntubi mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben APC, Kingsley Fanwo da kuma babban mataimaki na musamman ga gwamnan Kogi kan harkokin yada labarai, Michael Ozigi, kan ko dan takararsu zai sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, amma duk su biyun ba su amsa ba.
Haka shi ma, dan takarar jam’iyyar PDP, Dino Melaye bai amsa ba.
A Jihar Bayelsa
An kasa masun ‘yan takarar manyan jam’iyyun siyasa uku da mambobin majalisar yakin neman zabensu.
Hakan ya kasance ne sakamakon kara zafafa yakin neman zabe da jam’iyyu suke gudanarwa a dukkan kananan hukumomin jihar.
Dangane da matakan da hukumar zabe ke dauka na kare ma’aikatanta, shugaban sashen wayar da kan masu jefa kuri’a, Wilfred Ifogah, ya ce hukumar ta gudanar da tattaunawa da dama da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a zaben.
Ya ce, “INEC ba ta aiki ita kadai ba. Akwai kwamitin tuntuba tsakanin hukumomin tsaro kan harkokin zabe (ICCES). Wannan tawaga ce ta dukkan hukumomin tsaro da ake da su a zaben jihar. Kwamishinan zabe da kwamishinan ‘yansanda ne ke jagorantar tawagar a kwacce jiha.”
A cewarsa, duk wannan na faruwa ne domin tabbatar da cewa masu kada kuri’a za su kasance a rumfunan zabe ba tare da wata matsala ba.
Tuni dai ake ci gaba da samun rashin tsaro a wadannan jihohi da za a gudanar da zaben gwamna.
Yayin da zaben Kogi zai iya samun cikas da ayyukan ‘yan daba kamar yadda aka gani a zaben da ya gabata, masu zabe a Imo da jami’an INEC na iya samun kalubalan ‘yan bindiga.
Har ila yau, a Jihar Bayelsa lamarin na matukar tayar da hankali, inda wasu ‘yan bindiga da ake zargin makiyaya ne ke kai hare-hare kan manoma da fararen hula har ma da jami’an tsaro.
Ita ma hukumar zabe na iya samu matsaloli wajen gudanar da zaben, wadanda suka shafi kan kayan aiki a lungu da sako na jihohin da saka sakamakon zabe ta na’ura da dai sauransu.
Source LEADERSHIPHAUSA