Yanzu haka dai kallo ya koma kan Majalisar Dattawa dangane da batun nadin sabbin ministocin Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.
‘Yan Nijeriya na ta dakon ganin wadanda za a nada tun daga farkon watan nan na Yuli bisa yadda ake ganin gwamnatin kamar ta zo a shirye, za ta yi komai cikin hanzari a kokarinta na fara gudanar da aikace-aikace da ‘yan kasa za su gani-a-kasa.
Kamar yadda sashe na 42, karamin sashe na daya na tsarin mulkin Nijeriya ya fada, an bai wa Shugaba Tinubu wa’adin gabatar da sunayen ministocin daga ranar da aka rantsar da shi 29 ga Mayun 2023 zuwa ranar 28 ga Yuli. “Za a gabatar da sunan duk wanda ake son nadawa a mukamin minista ga Majalisar Dattawa domin tabbatarwa bayan kwana 60 da rantsar da shugaban kasa”.
Domin kawar da jiran tsammanin da aka dade ana yi, a ranar Talatar makon nan, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Micheal Opeyemi Bamidele ya tabbatar da cewa kafin karshen makon komai zai daidaita dangane da gabatar da sunayen sabbin ministocin.
A ‘yan makwannin da suka gabata dai, an yi ta yawo da wani jerin sunayen mutane a matsayin wadanda Tinubu yake son nadawa minstoci, sai dai mai magana da yawun shugaban kasan, Dele Alake ya bayyana sunayen a matsayin na bogi.
Hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki sun kammala duk binciken da suka kamata a kan sabbin ministocin.
Kamar yadda aka saba gani a gwamnatocin baya, Majalisar Dattawa za ta kwashe tsawon wasu kwanaki tana aikin tantance wadanda ake son nadawa ministocin. Inda wani lokaci ake watsawa kai-tsaye ta gidajen talabijin domin ‘yan kasa su shaida yadda lamarin ke gudana.
A yayin tantancewar dai, ‘yan majalisar ta dattawa kan gabatar da tambayoyi ga mutanen da aka mika sunayensu kan abubuwan da suka shafi asalin mutum, basira da kwarewar aiki, wani lokaci har da gudunmawar da mutum ya bayar ga jam’iyya mai mulki.
Haka nan ‘yan majalisar kan sauwake wa galibin wadanda suka taba zama ‘yan majalisa daga cikin sabbin ministocin, inda ba a musu tambayoyi sai dai a ce su yi gaisuwar girmamawa ga ‘yan majalisar su tafi. Lamarin da wasu masu fashin baki ke kallon son zuciya ne saboda ba duk wanda ya taba zama dan majalisa ba ne yake da basirar aiki musamman yadda wasu kan zama masu dumama kujera ba tare da gabatar da kudiri ko daya ba tun daga farko har karshen wa’adinsu na shekara hudu.
Bayan kammala tantance wadanda ake son nadawa ministocin dai, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu zai raba musu ma’aikatun da za su yi aiki inda ake sa ran a tura kowa ma’aikatar da ake ganin yana da basira da kwazon da zai iya tafiyar da ita domin kawo ci gaba.
Ministoci su ne kashin bayan gudanar da ayyukan gwamnati, saboda duk aikin da gwamnatin tarayya za ta gudanar a karkashinsu ne, su suke tsarawa su gabatar, shugaban kasa ya rattaba hannu a kai bayan an cimma matsaya a taron majalisar zartaswa ta kasa.
Tinubu ya yi alkawarin tafiyar da gwamnatin hadin kasa tare da jam’iyyun adawa da kuma bangarorin kwararru wadanda ba ‘yan siyasa ba, sai dai nade-naden mukaman da zai yi ne za su tabbatar da abin da ya fada ko akasin haka.
Source: Leadership Hausa