Sabbin hotunan matar shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari ya jawo tsegumi da cece-kuce tsakanin ‘yan Najeriya inda da dama ke cewa kamar tana da ciki.
A daya daga cikin hotunan da aka ganta tare da shugaba Buhari da dogarinta na rike da jaka, ‘yan Najeriya sun yi ta magana akan hoton.
Dayan Hoton kuma ya nuna Shugaba Buhari da Hajiya A’isha zaune wanda masu sharhin suka ce fuskarta ta yi kama da ta me ciki, wadda ba haka aka saba ganinta ba.
Wani me suna @promise ya tambayi cewa shin Hajiya A’isha na dauke da ciki ne ko kuwa menene muke gani haka?
Shima wani me sunan @Solowizzy ya bayyana cewa ‘yan Najeriya me kuke gani a wannan hoton? Ta bayyana cewa Hajiya A’isha na dauke da ciki.
Shi kuma wani me sunan @Alamin97296003 cikin barkwanci cewa yayi ina jinjinawa shugaba Buhari kan kokarinsa duk da yana dan shekaru 79.
Hakannan shima wani ya bayyana cewa, A’isha Buhari na da ciki, baba ya iya aiki.