Kakakin majalisar wakilan Najeriya ya dage zaman majalisar a fusace kan rashin jerin tsarin abubuwan da za a tattauna Femi Gbajabiamila ya isa majalisar inda ya tarar babu magatakarda a kujerarsa kuma ‘yan majalisar tsiraru ne suka bayyana.
A fusace ya dage zaman majalisar inda yace sai zuwa ranar Talata ta mako na gaba za su sake haduwa.
‘Yan majalisar wakilai sun kasa zama a ranar Alhamis bayan kakakin majlisar Femi Gbajabiamila ya dage zaman su zuwa mako mai zuwa a fusace.
Channels TV ta ruwaito cewa, kakakin majalisar ya hallara zauren majalisar wurin karfe sha daya da minti ashirin, a fusace kakakin majalisar ya dage zamansu sakamakon rashin takardar oda.
‘Yan majalisar wakilai sun kasa zama, a fusace kakaki ya dage zamansu.
Hakazalika ya fusata da magatakardan majalisar kan rashin ganin sa a majalisar yayin da ya iso.
Har ila yau, majalisar babu mutane saboda a lokacin da kakakin majalisar ya isa, ‘yan majlisa kadan ya tarar.
Daga nan ne kakakin majlisar ya dage zaman majalisar har zuwa ranar Talata ta makon gaba.
A wani labarin na daban Argentina ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin Duniya duk da rashin nasara a wasansu da Brazil na jiya talata da suka tashi babu kwallo amma rashin nasarar Chile da Uruguay ya taimakawa mata.
Argentina ita ce kasa ta biyu a kudancin Amurka da ta samu gurbin bayan Brazil da ta samu nata gurbin a farkon makon jiya.
Samun tikitin na Argentina ya mayar da jumullar kasashen da zuwa yanzu yanzu suka samu tikitin na zuwa Qatar guda 13.
Yanzu haka dai kasashen turai 10 ciki har da Portugal da kuma Italiya zakarar Euro ne za su yi dakon wasannin cike gibi gabanin samun tikitin na Qatar.