Kaftin din kwallon kafar Super Eagles ta Najeriya Ahmed Musa ya nemi gafarar magoya bayan su dangane da gazawar da suka yi lokacin karawa da kasar Tunisia a gasar cin kofin Afirka dake gudana a kasar Kamaru.
Kaftin yace sun bada kashi 100 na abinda za su iya yi wajen samun nasarar wasan, amma kuma basu samu nasarar da ake bukata ba.
Musa yace ba za suyi kasa a gwuiwa ba a gasa ta gaba, yayin da ya godewa ‘Yan Najeriya akan irin goyan baya da addu’oin da suka yi ta musu.
Kasar Tunisia ta doke Najeriya da ci 1-0 a zagaye na biyu na gasar cin kofin Afirka dake gudana a Kamaru, abinda yayi sanadiyar fitar kasar daga gasar.
Ana saran Najeriya ta kara da Ghana a zagayen karshe na neman tikitin zuwa cin kofin duniya a watan Marin mai zuwa.
A wani labarin na daban Tawagar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya ta lashi takobin lashe kofin gasar kasashen Afrika da za a fara gudanarwa daga ranar 9 ga wannan wata na Janairu a Kamaru zuwa 6 ga watan gobe na Fabairu.
Najeriya za ta yi wasanta na farko ne da Masar a rukunisu na D a ranar 11 ga watan nan, wasan da babu shakka zai dauki hankali matuka saboda zubin ‘yan wasan da kowanne bangare ke tunkaho da su.
Mohamed Salah na Liverpool ne zai jagoranci tawagar Masar wadda ta lashe kofin gasar Afrika har sau bakwai, yayin da Najeriya ta lashe sau uku, amma take fatan sake lashewa a karo na hudu.
Kodayake masana harkokin wasan sun fara hasashen yadda za ta kaya a fafatawar tsakanin kasashen biyu, inda Kamfanin Dillancin Labaran Faransa ke cewa, da yiwuwar Najeriya ta samu nasara kan Masar da ci 2-1.
Alkaluma sun nuna cewa, sau biyu kacal Masar ta doke Najeriya a daukacin wasannin da kasashen biyu suka yi a gasar ta cin kofin Afrika.