Kwanaki uku bayan da tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ba ya goyon bayan kowane ɗan i shugaban ƙasa a zaɓen 2023, shi ma takwaran sa Goodluck Jonathan ya ce kowa ta sa ta fis she shi, ba zai goyi bayan kowane ɗan takara ba.
Jonathan ya bayyana haka a Abuja wurin taron taya Babban Limamin Kirista, Mathew Hassan-Kukah murnai cika shekaru 70 da haihuwa.
A wurin taron an kuma ƙaddamar da gidauniyar gina Cibiyar Nazarin Nagartacciyar Gwamnati ta Hassan Kukah.
Jonathan ya bayyana matsayar sa kwanaki biyu bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu ya kai masa ziyara a gidan sa na Abuja.
A wurin taron Hassan Kukah, Tinubu da mataimakin takarar sa duk sun halarta, kuma a gaban su Jonathan ya ce babu ruwan sa da kowane ɗan takara.
A wani labarin na daban katafaren kamfanin makamashi na Gazprom na Rasha ya dakatar da isar da iskar gas zuwa Jamus, wanda shi ne na baya bayan nan da aka dakatar, abin da ya haifar da matsalar makamashi ga nahiyar Turai.
Gazprom ya kuma ce zai dakatar da samar da iskar gas ga babban kamfanin samar da iskar gas na Faransa Engie daga ranar alhamis bayan da ya gaza biyan basukan da ake bin sa a watan Yuli.
Tsagaitawar ta baya-bayan nan ta zo ne a daidai lokacin da kasashen Turai ke fuskantar hauhawar farashin makamashi tun bayan da Rasha ta mamaye kasar Ukraine a karshen watan Fabrairu, sannan ta dakile hanyoyin aika musu da iskar gas zuwa yankin.
Jamus wacce ta dogara da iskar gas daga Rasha, ta zargi kasar da amfani da makamashi a matsayin daukar fansa ga kasashen yamma.
Kungiyar Tarayyar Turai na shirin daukar matakin gaggawa domin yin garambawul ga kasuwar lantarki, domin shawo kan hauhawar farashin kayayyaki, inda ministocin makamashi za su yi wata tattaunawa ta musamman a mako mai zuwa.