Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya gargaɗi ‘yan Najeriya su yi takatsantsan wajen zaɓen shugabanni a 2023.
Jonathan yace duk ɗan takarar da ya ɗauki makami ya yi kisa don zama shugaba, haka zai ci gaba da aikata wa.
Ya kuma yaba wa gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, bisa dumbin ayyukan ci gaba da ya yi wa talakawansa.
Yayin da ake tunkarar babban zaɓe, tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya gargaɗi ‘yan Najeriya kar su yi kuskuren zaɓen wasu shugabanni da ya kira “Masu kisa” a zaɓen 2023.
Jonathan ya yi wannan gargaɗin ne ranar Lahadi a Uyo a wurin wani taron Addu’o’in godiya na musamman na bikin cikar jihar Akwa Ibom shekara 35 da kafu wa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
“A zaɓen 2023, ya zama tilas ku kula kada ku yi kuskuren zaɓen shugabanni masu aikata kisa, waɗanda ke ɗaukar wuƙaƙe, bindigu, da sauran makamai su kashe mutane saboda siyasa.”
“Idan ka kashe mutane don kawai ka zama shugaba, haka zaka ci gaba da kashe mutane don ka zauna a kujerarka.
Mutane zasu ci gaba da shan wahala ne kawai.”
“Ku tabbata tun daga majalisar dokokin jiha zuwa majalisar wakilan tarayya da Sanatoci da gwamna kun zabi mutane masu amana da aka yarda da su a jihar Akwa Ibom.” – Goodluck Jonathan.
Jonathan ya yaba wa gwamnan Akwa Ibom Tsohon shugaban ƙasan ya yaba wa gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom bisa yadda ya ba mara ɗa kunya wajen ayyukan cigaba a jihar da ke kudu maso kudancin Najeriya.
Ya haƙaito lokacin da tsohon gwamna, Godswill Akpabio, ya bar Ofis, an yi hangen rashin tabbas game da kokarin gwamna Emmanuel, wanda a lokacin yana Sakataren gwamnati.
Duk da Udom Emmanuel ya shiga siyasa ne daga ɓangaren masu cin gashin kansu, Jonathan yace gwamnan ya yi abinda ya dace a shekara Bakwai da hawa madafun iko, Premium Times ta ruwaito.
A wani labarin kuma Tsohon Sakataren Buhari Ya Fallasa Wasu Kulle-Kullen da Tinubu Ke Yi Gabanin 2023 Tun farko dai dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya nuna cewa dalilinsa na zabar musulmi a matsayin abokin takara ba saboda addini bane.
Babachir David Lawal ya zargi Tinubu da kulla-kulla da son raba kan mabiya addinin kirista a kokarinsa na shawo kan mutane su yarda da shi.
Source: LEGITHAUSA