Gwamnatin Jihar Katsina ta dauki jami’an kiwon lafiya sama da dubu daya aiki domin bunkasa kiwon lafiya a jihar. Gwamna Aminu Bello Masari ne ya sanar da hakan cikin sakon da ya aike da shi wajen taron shekara-shekara wanda kungiyar likitoci ta kasa reshen Jihar Katsina ta shirya.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Lafiya, Injiniya Yakubu Nuhu Danja, ya yi bayanin cewa a duk shekara gwamnati na daukar nauyin likitoci 78 domin karo karatu a ciki da wajen kasar nan. Kamar yadda ya ce gwamnatin jihar ta kafa hukumar kula da lafiya matakin farko da hukumar taimakekeniyar kiwon lafiya ta jiha da kuma hukumar samar da magunguna ta jiha da nufin bunkasa kiwon lafiya a jihar.
Alhaji Aminu Masari ya yaba ma kungiyar likitocin a kan gudanar da tiyata ga marasa lafiya kyauta, ya amince da bai wa kungiyar fili domin gina ma ‘ya’yanta gidaje.
Gwamnan ya ce zuwa yanzu mutane akalla 2160 ne aka tabbatar sun harbu da cutar Korona a katsina. Ya kuma kara da cewa an samu wadanda suka kamu da cutar amai da gudawa a jihar sama 1000, sama da mutum sittin kuma sun rasu sakamakon annobar. Ya ce gwamnatin na yin bakin kokarinta domin ganin an magance matsalar.
Da yake jawabinsa, shugaban kungiyar likitoci ta kasa reshen Jihar Katsina, Dakta Abubakar Dahiru ya bayyana cewa kungiyar ta gudanar da aikin tiyata kyauta ga marasa lafiya akalla 40 a babban asibitin Kankiya. Ya ce kungiyar ta kuma bayar da magunguna tare da duba wasu da ke tsare gidan gyara halinka kyauta.