Tsohon dan takarar gwamna kuma jigon siyasa ya bayyana kadan daga alheran tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Jigon na siyasa ya ce, Obasanjo ya fi Tinubu, Buhari da dukkan jiga-jigan APC a hade a komai da komai.
Ana kai ruwa rana tsakanin jiga-jigan APC da kuma masu goyon bayan Peter Obi da Obasanjo a wannan makon.
Jigon jam’iyyar Labour a jihar Legas, Babatunde Gbadamosi a ranar Takata ya caccaki jam’iyyar APC mai mulki kan tabo toshon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
A makon nan ne tsohon shugaban kasa Obasanjo ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, Tribune Online ta ruwaito.
Awanni bayan bayyana goyon bayansa ga Obi, tawagar kamfen ta APC ta ce Obasanjo ya ji kunya, kuma yana da rauni a fannin siyasa.
A bangare guda, fadar shugaba Buhari ta caccaki Obasanjo, inda tace Buhari ya fi alheri ta kowane bangare.
Da yake martani, tsohon dan takarar gwamnan jihar Legas a jam’iyyar ADP ya yi rubutu a Twitter, inda ya caccaki APC da fadar Buhari tare da cewa, Obasanjo ya fi kowa a jam’iyyar APC.
A cewarsa: “Na ambata a 2019 cewa, girman karamar yatsar Obasanjo ta zarce ta Tinubu, Buhari da dukkan shugabannin APC idan aka gwama.
Har yau dinnan gaskiya ne.” Kishi suke da Obasanjo Hakazalika, ya bayyana cewa, masu sukar Obasanjo ba don komai suke hakan ba sai don kishi da irin nasarori da ya samu na rayuwa.
A cewarsa, inda Obasanjo ya taka basu isa zuwa wurin ba, don haka suke hassada da karbuwarsa a idon duniya, News Direct ta tattaro.
Daga karshe ya shaida cewa, ba laifi bane a ce mutum mai karimci kamar Obasanjo ya goyi bayan Peter Obi ba, domin duk suna da mustawa mai kyau.