Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara ta karbi wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP da jam’iyyar NNPP a jihar.
A ranar Litinin ne tsohon Gwamna kuma shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamna na jam’iyyar APC a jihar, Abdul’aziz Yari ya karbe su.
Mai magana da yawun Yari, Dahiru Mafara ne, ya bayyana sunayen mutanen a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Jiga jigan su ne Ibrahim Shinkafi, dan takarar Sanata na jam’iyyar NNPP mai wakiltar mazabar Zamfara ta Arewa; Dan takarar majalisar wakilai, Shinkafi da Zurmi, Suleiman Garba.
Ma’ajin Jihar, Suleiman Galadi; Su ma shugabannin NNPP na kananan hukumomin Kaura-Namoda da Zurmi sun sauya sheka.
Yari ya samu wakilcin shugaban kwamitin tuntuba da wayar da kan jama’a na kwamitin, Musa Zubairu.
Taron wanda ya gudana a Talatan Mafara, ya samu halartar shugaban jam’iyyar APC na Zamfara, Tukur Danfulani da sauran masu ruwa da tsaki.
A wani labarin na daban BBC ta ce, Masu garkuwa da mutane sun kashe wasu ‘yan uwan juna su uku tare da wani mai babur bayan da suka karɓi fansar naira miliyan 60 daga mahaifin yaran a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Nijeriya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a kusa da dajin Garin Dogo a yankin ƙaramar hukumar Lau ranar Lahadi.
Rahotonni sun ruwaito cewa masu garkuwar sun kama mutanen uku – waɗanda suke uwa ɗaya uba ɗaya – inda kuma suka buƙaci naira miliyan 100 a matsayin kuɗin fansa.
Mahaifin yaran uku wanda mai sana’ar safarar shanu ne ya daidaita da masu garkuwar – waɗanda suka amince zai biya su naira miliyan 60 domin sakin ‘ya’yan nasa uku.
Sai kuma ya ɗauki Ɗan Achaba tare da bashi kuɗin domin kai wa masu garkuwar a cikin dajin da ke kusa da ƙauyen nasu, dan sakin ‘ya’yan nasa.
To sai dai bayan kai kuɗin fansar da mai babur ɗin ya yi sai suka kashe shi tare da sauran yaran uku, bayan sun karɓi kudin fansar.