Yayin da ake kasa da sauran kwanaki 100 zaben shugaban kasar Najeriya, wani rahoton jaridar ThisDay yayi hasashen jerin jihohin da manyan takara uku ke bukatan ci.
Yan takaran sun hada da Bola Tinubu na APC, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP. Rahoton ya yi bayanin jihohin da ya wajaba wanda ke son nasara cikin wadannan yan takara uku yayi nasara idan har yana non zama shugaban kasa.
Game da Tinubu, rahoton ya lissafo jerin jihohin da ya wajaba ya samu kashi 60% da kuma 40% da kuma yiwuwan samun hakan.
Jerin jihohin da ya wajaba Tinubu ya samu akalla 60% idan yana son zama shugaba
Ya Wajaba Tinubu Yaci 60% Yiwuwan hakan Lagos Ana Sa rai, Ogun.
Ana Sa rai Ondo
Ana Sa rai Oyo Da Yiwuwa (Sai Ya Dage)
Osun Da Yiwuwa
Ekiti Ana Sa rai
Kano Da Yiwuwa (Kamar Wuya)
Kaduna Da Yiwuwa (Sai Ya Dage)
Katsina Da Yiwuwa (Sai Ya Dage)
Zamfara Ana Sa rai
Borno Ana Sa rai
Yobe Ana Sa rai Jerin jihohin da ya wajaba Tinubu ya samu akalla 40% idan yana son zama shugaba Jihohin da.
Ya Wajaba Tinubu Yaci 40% Yiwuwan hakan
Sokoto Ana Sa rai
Kebbi Ana Sa rai
Jigawa Da Yiwuwa
Benue Da Yiwuwa (Kamar Wuya)
Kogi Ana Sa rai
Niger Ana Sa rai
Kwara Da Yiwuwa
Plateau Da Yiwuwa
FCT Da Yiwuwa
Abin lura: Mafi akasarin jihohin dake karkashin mulkin APC yanzu ake sa ran Tinubu zai samu rinjaye.
Hakazalika Mafi akasarin jihohin dake karkashin mulkin PDP yanzu ake sa ran Tinubu sai ya yi da gaske.
Source:Legithausa