TA FARU TA KARE: Jam’iyyar APC Ta Fitar Da Sharudan Tsayawa Takarar Shugaban Kasa A Zaben 2023
Jam’iyyar APC mai mulki ta yanke matsaya kan batun fitar da dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023
Jam’iyyar APC tace:
(1) Duk wanda zai tsaya takaran shugaban kasa a jam’iyyar APC dole ya fito daga yankin kudancin Nigeria
(2) Mataimakin shugaban kasa zai fito daga Arewacin Nijeriya
Idan APC taci zaben 2023:
(3) Shugaban majalisar Dattawa zai kasance daga yankin kudu
(4) Mataimakin shugaban majalisar Dattawa zai fito daga yankin Arewa
(5) Kakakin majalisar wakilai na tarayya zai fito daga yankin Arewa
(6) Mataimakin kakakin majalisar wakilai zai fito daga yankin kudu
(7) Shugaban Jam’iyyar APC zai fito daga yankin Arewa
(8) Sakataren Jam’iyyar APC zai fito daga Kudu
(9) Ma’ajin kudin jam’iyyar APC zai fito daga kudu
(10) Sakataren kudin jam’iyyar APC zai fito daga Arewa
(11) Mai kula da sashin shari’ah zai fito daga Arewa
(12) Mai kula da jin dadi da walwalar jam’iyyar APC zai fito daga kudu
(13) Babban mai bincike na jam’iyyar zai fito daga Arewa
(14) Shugaban matasan jam’iyyar APC zai fito daga yankin kudu
(15) Shugaban matan jam’iyyar APC zata fito daga yankin kudu
(16) Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC zai fito daga yankin kudu
(17) Shugaban nakasassun mutane na jam’iyyar APC zai fito daga yankin kudu
Yanzu dai a APC ta haramtawa ‘yan Arewa tsayar da dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar inda ta yanke hukuncin mika kujeran zuwa ga yankin kudu
Jagoran jam’iyyar APC Alhaji Bola Ahmad Tinubu ko Professor Yemi Osibanjo a cikin wadannan mutane guda biyu daga yankin kudancin Nigeria APC zata zabi daya
Amma sai ina ganin kamar wannan matsaya na APC da ta fitar lissafi ne gurgu, sannan babbar damace ga jam’iyyar PDP ta karbi mulki idan ta tsayar da Dan Arewa takaran shugaban kasa
Muna fatan duk wanda zai zama alheri ga Kasarmu Nijeriya Allah Ya bashi.
Daga Datti Assalafiy