Jam’iyyar Shugaban kasar Afrika ta Kudu ta sha kayi a zaben wakilan hukumomin. Wannan dai ne karo na farko da jam’iyar marigayi Nelson Mandela ta fuskanci irin wannan kaye ,tareda samun kasar da kashi 50 cikin dari na sakamakon zaben da ya gudana.
Da samun wannan labari,kwamityn zartawa na jam’iyyar ANC ya kira taron gaggawa da wakilan jam’iyyar da nufin tattaunawa dangane da makomar jam’iyyar a wannan lokaci.
A wani labarin na daban shugaban Kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa ya caccaki kasashen da ke boye maganin rigakafin cutar korona yayin jawabinsa a wajen taron tattalin arziki na Duniya da ke gudana a Davos inda ya ce sam manyan kasashe basa damuwa a kananu a halin da ake ciki.
Shugaban ya bukaci wadannan kasashe da su saki maganin da basa bukata domin ganin kasashe marasa karfi sun amfana da su wajen yiwa jama’ar su rigakafi.
Afrika ta kudu ce kasar da Coronavirus ta fi yiwa barna a nahiyar Afrika, inda har yanzu al’ummarta ke karkashin matakan takaita walwala don dakile yaduwar cutar.