Har yanzu ba a nada sabon babban hafsan sojojin Najeriya ba, biyo bayan mutuwar Janar Attahiru kuma babu tabbaci wanda zai maye gurbin sa cikin jami’an sojojin.
Ana yada jita-jitar cewa, an nada wani sabon babban hafsan sojojin Najeriya, sai dai ba tabbatar da lamarin ba.
Ana sa ran wasu manyan jami’ai na daga cikin wadanda daya zai maye gurbin marigayi Janar Attahiru Fiye da awanni 24 bayan rasuwar babban hafsan sojan kasa, Laftanal-Janar Ibrahim Attahiru a wani hatsarin jirgin sama, har yanzu fadar shugaban kasa ba ta ambaci sunan wanda zai maye gurbinsa ba yayin da al’ummar kasar ke jimamin wadanda suka mutu.
Shugaba Muhammadu Buhari, yayin jana’izar mamatan da suka mutu a ranar Asabar, ya ce Laftanal-Janar Attahiru ya kasance gwarzo mai jarumtaka wanda har ya kai ga nada shi babban hafsan sojojin Najeriya, PRNigeria ta ruwaito.
Ministan tsaro na Najeriya, Manjo Janar Bashir Magashi ne ya wakilci shugaba Muhammadu Buhari a wajen jana’izar marigayi Attahiru, in da ya bayyana jimamin shugaban kasan da kuma jinjinawa aikin marigayin a fafutukar yaki da ta’addanci a Najeriya.
Ana yada jita-jitar cewa, bayan rasuwar Janar Attahiru, an ba Manjo Janar Danjuma Ali Keffi matsayin riko na babban hafson sojin Najeriya, wanda har yanzu ba a tabbatar ba.
Sai dai, an tattaro cewa Janar Keffi daga jihar Nasarawa ba ya cikin manyan hafsoshin sojan Najeriya.
A zahiri, akwai manyan jami’an sama da 30 da ke sama dashi, Saboda haka, wani babban hafsan soji ya bayyana cewa ana la’akari da dalilai da yawa wajen nadin shugabannin rundunoni da manya a gidan soja.
“Kun san Shugaban kasa yana da ikon nada duk wanda yake so tare da shawara ko wata kila daga Ministan Tsaro.”
Jami’in ya ce “Baya ga girman mukamai a cikin aikin, jami’an da ake yin la’akari da su tabbas su kasance suna cikin ayyukan soja da leken asiri.
Daga rahoton na PRNigeria, ga jerin manyan jami’an da ake sa ran daya daga cikinsu watakila ya maye gurbin marigayin kasancewarsu manyan jami’an rundunar soji.
1. Manjo Janar Ben Ahanotu daga jihar Anambra Shi ne Kwamandan rundunar Sojoji da suka kame wanda ya kafa kungiyar Boko Haram Mohammed Yusuf da mabiyansa a maboyarsu a Maiduguri a shekarar 2009 kuma ya mika su ga ’yan sanda.
2. Manjo Janar AM Aliyu daga jihar Gombe Shi ma wani babban jami’i ne. Shi ne Shugaban Gudanarwa na Sojojin Najeriya kuma tsohon Daraktan hulda da kasashen waje a Hukumar Leken Asiri ta Tsaro. Ya kasance mai alhakin sarrafa bayanan sirri na ayyukan soja.
3. Manjo Janar Ibrahim Manu Yusuf daga jihar Yobe Shi ne Babban Jami’in Tsaro kuma tsohon Kwamandan Rundunar Soja na Hadin gwiwa ta Multinational Joint Taskforce (MNJTF).
Ya kuma kasance tsohon Kwamandan Operation Lafiya Dole tare da gogewa a fagen yaki da ta’addanci da ayyukan tayar da kayar baya a yankin Arewa maso Gabas. Ya kuma koyar a kwalejojin soja da yawa ciki har da NDC, NDA da sauransu.
4. Manjo Janar Faruk Yahaya daga jihar Zamfara Shi ne kwamandan yaki a yanzu a Arewa maso Gabas kuma tsohon Babban Kwamandan Runduna ta 1 na jami’an Sojojin Najeriya.
A wani labarin, Yayin da ake jana’izar Janar Ibrahim Attahiru, Shugaban hafsan soji, da wasu 10 da suka mutu a hatsarin jirgin sama a Abuja, gwamnoni da yawa sun hallara zuwa Kano don halartar bikin dan Abubakar Malami, Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a.
Wannan ya haifar da cece-kuce daban-daban daga ‘yan Najeriya wadanda ke ganin manyan jami’an sojojin da suka mutu a bakin aiki ba su sami irin girmamawar da ta dace da su ba. Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ba su halarci jana’izar ba wacce ta samu halartar Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan.