Jami’an diflomasiyya na halartar taron hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya kan bukatar tsaurara matakan sa ido kan halin da mutunta hakkin dan adam ke ciki a Sudan, biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a makon da ya gabata.
Har ila yau, kudurin yayi tir da yadda sojojin a karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah Al Burhan suka hambarar da Firaminista Abdallah Hamdok da wasu mukarrabansa tare da tsaresu bayan juyin mulkin, ko da ya ke daga bisani sun sake su.
Muhawara kan halin da Sudan ke ciki na zuwa ne bayan da Janar Al Burhan ya ba da umarnin sakin wasu ministoci hudu da ake tsare da su tun bayan da sojoji suka karbe mulki.
Juyin mulkin da aka sake yi a Sudan ya janyo cece-ku-ce gami daga kasashen duniya, musamman ma bayan da jami’an tsaro suka yi amfani da karfi wajen yunkurin murkushe gagarumar zanga-zangar da dubban ‘yan kasar ke yi na nuna adawa da sojoji, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane akalla goma tare da jikkatar wasu fiye da 300.
A wani labarin na daban shugaban sojin Kasar Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan ya bada umurnin sakin 4 daga cikin ministocin tsohuwar gwamnatin rikon kwaryar da ya kawar a makon jiya.
Sanarwar da gidan talabijin din Sudan ya sanar ta bayyana ministocin da aka bada umurnin sakin su da suka hada da Hashem Hassan Alrassoul da Ali Geddo da Hamza Baloul da kuma Youssef Adam.
Alrasoul ya jagoranci ma’aikatar sadarwa, Geddo ma’aikatar ciniki, Baloul ma’aikatar yada labarai, sai kuma Adam da ya rike ma’aikatar wasanni.
Babu wata sanarwa dangane da makomar tsohon Firaminista Abdallah Hamdok.