Wasu rahotanni na nuna yiwuwar sojin da ke mulki a Jamhuriyar Nijar za su iya amincewa da sakin hambrarren shugaban kasar, Mohamed Bazoum da iyalinsa kowanne lokaci daga yanzu.
Rahotannin sun bayyana cewar akwai yiwuwar cimma matsaya kan sakin shugaban a cikin watan Ramadan.
A cewar bayanan har yanzu akwai dambarwar dangane da bukatar Bazoum ya ci gaba da zama a Jamhuriyar Nijar ba tare da fitarsa kowace kasa ba, wanda shi ne dalilin da ya kai ga gaza sakinsa har a wannan lokaci.
Bazoum dai na samun cikakken goyon bayan shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron da kuma kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS).
Hakan ya sa ana ganin shi ya sake tsaurara matakan sakin nasa daga sojojin da suka yi juyin mulki a kasar.
Tun bayan hambarar da gwamnatin ta Bazoum Mohamed a watan Yulin 2023, Nijar ta fuskanci takunkumai daga Faransa da ECOWAS, lamarin da zafafa alaka tsakanin Nijar da Nijeriya.
DUBA NAN: Arewacin Najeriya Na Fama Da Sace Sacen Yara
Baya ga Nijar ECOWAS ta kuma kakaba wa Mali da Burkina Faso wadanda ke fuskantar mulkin soji, takunkumai.
A wani labarin na daban Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci nan da mako biyu zuwa uku a samar da maslaha kan rikice-rikicen manoma da makiyaya a fadin kasar nan.
Shugaba Tinubu ya bukaci gwamnonin jihohi da su samar da filayen kiwo ga makiyaya a jihohinsu don warware matsalolin da suka addabi bangarorin biyu.
Tinubu ya bayyana hakan ne a Minna, babban birnin Jihar Neja, a yayin da yake kaddamar da shirin noman zamani domin samar da wadataccen abinci a Nijeriya.
Kazalika, ya bukaci gwamnoni da su hada karfi da karfe domin kawo karshen matsalar abinci.
Rikicin manoma da makiyaya ya dade a Nijeriya, lamarin da ya kai ga salwantar rayuka masu yawa da tarin dabobbi.
Har wa yau, matsalar ta wanj bangare na da alaka da samar da ‘yan fashin daji, wadanda suka rikide zuwa mahara masu satar mutane domin neman kudin fansa.
A gefe guda kuma matsalar ta zama silar hana manoma da dama yin noma a gonakinsu, lamarin da ke barazana da samar da abinci a kasar nan.