Tun biyo bayan kubutar wasu falasdinawa shidda daga kurkukun haramracciyar kasar isra’ila, wanda ke da tsaatstsauran tsaro.
Tun bayan da falasdinawan suka iya kubuta daga gidan yarin na israila an shaidi sabbin hare hare, kamu, cin zarafin dan adam gami da kai samamen dare kan raunana falasdinwa a yankin ”west bank”.
Kamfanin yada labaran falasdinu na wafa newas ya tababbatar da cewa a ranar larabar da ta gabata sojojin haramtacciyar kasar isra’ila sun kama falasdinawa shidda wadanda basu ji ba basu gani ba a wani samamen dare da sojojin haramtacciyar kasar isra’ilan suka kai yankin na west bank da tsakar dare.
Gwamantain haramtacciyar kasar isra’ila dai bata bayanin dalilan hare haren da take kai wa, kuma bata sanar da sahihancin wadannan hare hare balle tayi bayanin dokar da ta bata damar aiwatar da wadannan hare haren ta’addanci.
Kamfanin yada labari na wafa newa ya tabbatar da cewa hare haren a kan aiwatar dasu ne a yankunan ke karkashin ikon falasdinawa wanda hakan ke nuna haramcin aiwatar wadannan hare hare a fili.
Wafa news ta cigaba da cewa a dokar isra’ila, sojojin su suna da damar daukan matakan, shari’a, gudanarwa da kuma tabbatar da doka a kan falasdinawan da suka kai miliyan daya, wannan kuma su falasdinawa basu da masaniya kan yadda sojojin na isra’ila zasu ke gudanar da wadannan damarmaki.
A ranar laraban dai sojojin isra’ila sun fada yankin jenin wanda yana karkashin ikon falasdinawa inda suka kaddamar da wasu hare haren kuma suka sanya shingayen binciken masu wucewa wanda hakan ya sabawa doka.
Kusan kungiyoyin kare hakkin dan adam 200 ne suka nuna damuwar su dangane da wadannan hare haren na hamatacciyar kasar isra’ila kuma suka zargi kasar da laifin kokarin salwantar da rayuwar falasdinawa shidda wadanda sojojin ta suka kama daga baya.
Gwamnatin isra’ilan dai na kallon wadannan hare haren nata a matsayin nasara amma sai dai al’ummomin duniya na kallon hakan a matsayin bakin zalunci.