Dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran wadanda aka fi sani da IRGC sun bayyana cewa zasu mayar da martani mai zafi kan duk wanda yayi kokarin taka jan layin kasar ta Iran.
Dakarun na IRGC sun tabbatar da cewa duk wani kuskure karami ko babba wanda ya taka jan layin kasar su, zasu tabbatar bai tafi hakanan ba a wani salo na jan kunnen masu yunkurin aikata wasu ayyuka da suka saba dokokin kasa da kasa.
Rundunar IRGC ta sanar da hakan ne a wani taron jami’an tsaro da aka gudanar a Iran din, inda tace ta hada hannu da sauran ciboyoyin tsaron Iran din domin tabbatar da, tsaro, yanci da da kudurorin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran din.
Sanarwar ta cigaba da cewa dakarun na IRGC zasu cigaba da gudanar da ayyukan su yadda ya kamata ba tare da lura da kalaman da gwamnatin ‘yan ta’adda ta amurka ke fada dangane da dakarun ba.
Zarge zargen da gwmantin amurka ke saki a kan dakarun na IRGC suna nuna yadda shugabannin amurkan suka kasa tabuka komi dangane da abinda ke faruwa da rugujewar tasirin amurkan a nahiyar asiya dama sauran bangarorin duniya.
Makaman mizayil da kuma tasirin da jamhuriyar musulunci ta samu a yankin asiya na cikin bangaren jan layin Iran, kamar yadda rahoton ya bayyana.
Manyan jami’an gwamnatin Iran sun sha nanatawa cewa Iran din ba zata daga kafa ba wajen tabbatar da tsaron kasar ta kuma masana’antar mizayin na cikin jan layin jamhuriyar musuluncin ta Iran wanda bazai yiwu a sanya ta cikin kowacce irin tattaunawa ba
Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran ma, Ayatullah Sayyid Ali Khamene’e ya jaddada bukatar Iran din ta kara inganta tsaron ta domin tsira daga barazanar makiya.
Iran dai na cikin kasashe masu tashen karfin tsaro a fadin duniya a halin yanzu, lamarin da amurka ke gani a matsayin barazana gareta.