Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya buƙaci al’ummar jihar su ci gaba da gudanar da ayyukan su na ibadah da suka yi a watan na Ramadana, da addu’o’in zaman lafiya da ci gaban jihar da Nijeriya baki daya.
Gwamnan ya yi wannan kiran ne a sakon sa na Barka da Sallah da Ismaila Uba Misilli, hadiminsa a bangaren yada labarai da hulda da jama’a ya fitar.
Gwamna Inuwa, wadda ya bayyana sallar Eid-el-Fitr a matsayin lokacin tunani da nazari kan rahamomin Allah ga bayi, ya bukaci al’ummar Musulmi su rinka dabbaƙa darusan da suka koya a watan na Ramadan a rayuwar su ta yau da kullum.
Ya ce, “Yayin da muke bukukuwan Eid-el-Fitr, ina yi mana nasiha da mu yi koyi da kyawawan darussa na watan Ramadan wadanda suke nuni da takawa, da biyayya, da sadaukarwa. Dole ne dukkan mu mu yi koyi da koyarwar Musulunci da ke tabbatar da zaman lafiya da hakuri, da kana’a da kuma kauna”.
Gwamna Inuwa ya kuma bukaci al’ummar jihar da cewa kar su sare game da kalubalen zamantakewa da na tattalin arziƙin da ake fuskanta a kasar nan, amma su jajirce wajen yin addu’o’i, yana mai cewa idan suka jajirce, jarabawar da ake ciki za ta wuce, kuma Nijeriya za ta kara karfi da karsashi da hadin kai.
Ya kuma bukaci jama’a su ci gaba da ririta zaman lafiya da kwanciyar hankali da ake da shi a jihar, inda ya yi kira ga malamai da sarakuna su ci gaba da wa’azin hadin kai da hakuri a tsakanin al’ummomi daban-daban don samun zaman lafiya da ci gaban Jihar Gombe da kasa baki daya, yana mai bayyana zaman lafiya a matsayin ginshilin ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin kowace al’umma.
Gwamna Inuwa, ya kuma jaddada cewa gwamnatin sa ba za ta lamunci duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya da ake da shi a jihar ba, kuma zata ci gaba da mai da hankali wajen ganin an samar da ribar demokradiyya ga al’ummar Jihar.
Sai ya yi kiran yin addu’o’i na musamman ga shugabanni a kowane mataki. “A irin wannan muhimmin lokaci na sauyin mulki da za a yi a kasar mu nan bada dadewa ba, ina kira a gare mu dukka, mu yi ta addu’a domin samun sauyin cikin kwanciyar hankali, musamman ma ga shugabanni masu zuwa a mukamai daban-daban, domin Allah ya basu hikima ya kuma yi musu jagora wajen sauke nauyin da ke kan su”.
“Ina mika godiya ta ga sarakuna da shugabannin al’umma da malaman addini da kuma dokacin al’ummar Jihar Gombe bisa goyon bayan da suke bai wa gwamnatin mu. Ina kira a gare mu, da mu sake sadaukar da kan mu, mu bada kyakkywar gudumawa ga ci gaban jihar mu. Ina mai tabbatar muku cewa gwamnatin mu ta himmatu wajen ganin Jihar Gombe ta samu ci gaba cikin sauri da kuma dorewar ci gabanta baki daya.”