Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta yanke shawarar yin aiki da na’urar rajistar masu zaɓe ta zamani ne wajen aikin rajistar masu zaɓe saboda zurfafa aiki da fasahar zamani a tsarin.
Babban kwamishina kuma shugaban kwamitin wayar da kan masu zaɓe da yaɗa labarai a INEC, Mista Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a lokacin wata tattaunawa da ya yi da Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) a ranar Litinin a Abuja.
Ya bayyana cewa na’urorin, mai suna ‘Voter Enrolment Device’ (VED), wadda an ƙirƙire ta bisa tsarin ‘android’ na ƙaramar komfuta ta ‘tablet’, za a kawo su ƙasar nan a ranar Litinin, 31 ga Mayu, domin a soma aiki da su a wajen rajistar masu zaɓe a ranar 28 ga Yuni.
Okoye ya ce Hukumar Zaɓe (INEC) ta daina aiki da tsohuwar na’urar nan mai suna ‘Direct Data Capture Machine’ (DDCM) wadda aka yi aiki da ita a ayyukan rajista da aka yi a baya, kuma yanzu za a maye gurbin ta da sabuwar na’urar.
Ya ƙara da cewa na’urar ta VED za ta bada damarmaki da dama, waɗanda su ka haɗa da kyakkyawar hanyar gane fuskar mutum da zanen hannun mutum kai-tsaye.
Babban kwamishinan ya ce wasu damarmakin kuma su ne daɗin ɗauka da sarrafawa, da kuma “daidaituwa da buƙatun Katin Shaidar Ɗan Ƙasa.”
Ya ce, “Na’urar VED ta bambanta da ta DDC, domin babban ƙullutun aikin DDCM, wato komfutar laptop, an maye gurbin ta da ƙaramar komfutar ‘tablet’.
“Na’urar ta fi daɗin ɗauka fiye da ta DDCM. Na’ura ce ta zamani saboda ɓangarorin ta an yi su ne da fasahohin da aka inganta tare da sabunta su fiye da na DDCM.
“A yanzu da lokacin fara aikin ya ƙarato, Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, zai yi wa mutanen ƙasar nan ƙarin bayani kan hanyoyin da aka tsara na fara aikin da kuma yawan cibiyoyin da aka tanadar wa ‘yan Nijeriya.’’
Okoye ya ce saboda kiyayewa da sashe na 10(2) na Dokar Zaɓe ta 2010 (wadda aka gyara), INEC za ta yi amfani da hanyar gamin gambiza ta aikin rajista ido da ido da kuma ta yanar gizo.
Ya ce, “‘Yan Nijeriya waɗanda ba su iya komfuta ba ko waɗanda ke zaune a yankunan karkara za su iya fara rajistar su har su gama a kowace daga cikin cibiyoyin rajista da aka tanadar.
“Waɗanda ke da komfuta ko ‘tablet’ ko babbar wayar hannu za su iya fara yin rajistar su ta hanyar yanar gizo kuma su kammala shigar da bayanan su a kowace daga cikin cibiyoyin da aka ware.
“Gidan yanar zai kasance ya na da ɓangaren yin rajista da alamar da ke nuna wurin yin zaɓe waɗanda za su taimaka wa masu yin rajista wajen sanin wurin da za su yi rajista da wurin yin zaɓe mafi kusa da su.”
Okoye ya ce Yakubu zai bayyana wa ‘yan Nijeriya yawan rumfunan zaɓe da na wuraren yin zaɓe na unguwa waɗanda aka mayar cikakken rumfunan zaɓe masu zaman kan su, da jimillar rumfunan zaɓe da ake da su a duk Nijeriya.
“INEC ta karya ƙwarin wata matsala da ta shafe shekaru 25 ana fama da ita wadda ta danganci ƙara yawan rumfunan zaɓe, kuma ‘yan Nijeriya za su samu damar sababbin rumfunan zaɓe.
“Rumfunan zaɓen za su bada dama ga naƙasassu da mata masu ciki da tsofaffi su samu damar yin zaɓe ba tare da wata wahala ba.
“Irin waɗannan rumfunan zaɓen za su kasance masu sauƙin isa gare su, da kuma sauƙin sarrafawa. Za su samar da damar yin tazara da juna kuma za su ba ma’aikatan mu na wucin gadi damar yin aikin da doka ta rataya masu a wuya cikin sauƙi.’’
Okoye ya ce rajistar masu zaɓe babban ginshiƙin tsarin dimokiraɗiyya ne, domin za ta ba ‘yan Nijeriya waɗanda su ka kai shekarun da kundin tsarin mulki ya amince masu da su yi rajista su yi amfani da ‘yancin su na dimokuraɗiyya.
“Saboda haka, ‘yan Nijeriya da su ka kai wannan zango na tsarin mulki da dokar ƙasa na yin rajista za su samu damar yin rajista.’’
Ya ce a taron da ya yi da manema labarai a ranar 1 ga Afrilu, Yakubu ya faɗi cewa rajistar masu zaɓe wata dama ce ga dukkan ‘yan Nijeriya waɗanda su ka kai shekara 18 da haihuwa kuma ba su taɓa yin rajistar yin zame ba.
Jami’in hukumar ya ce za kuma a bada dama ga kowane mai rajista wanda ke da wani kuka a lokacin ɗaukar bayanai a zaɓuɓɓukan da aka yi a baya, saboda hukumar ta gyara duk wata matsala.
Ya ce, “Dukkan masu zaɓe da aka yi wa rajista waɗanda ke so su sauya wurin jefa ƙuri’ar su zuwa wani wajen; da masu zaɓe da aka yi wa rajista waɗanda su ka ɓatar da katin su na zaɓe (PVCs) ko waɗanda katin su ya lalace, duk za a ba su dama.
“Haka su ma dukkan masu zaɓe da ke da rajista waɗanda ke so su yi gyara kan bayanan su kamar rashin rubuta suna a daidai ko kwanan watan haihuwa, da sauran su.”