Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce ta cire rumfunan zabe 749 daga wuraren da ba su dace ba a duk fadin kasar nan.
Masu sa ido kan rumfunan zabe na hukumar sun ce an cire tara daga cikin wuraren bauta tare da wasu da yawa daga gidajen addini, da gidajen sarauta, da gidaje masu zaman kansu.
Da yake magana a Abuja a wani taron ganawa da Kwamishinonin Zabe (RECs), shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce daga cibiyoyin kada kuri’u na farko 119,973, yanzu al’ummar kasar nan na da rumfunan zabe 176, 846 cikakku.
Hakan yana zuwa ne a dai dai lokacin da ake ta fuskantar kai hare hare a ofisoshin hukumar zaben ta INEC inda hakan ke sanya shakku dangane da tabbacin gudanar da zabe a shekarar 2023.
An jiyo shugaban kasa Muhammadu Buhari yana cewa duk tsananin yanayi dole za’a gudanar da zaben 2023 amma hakan ya sanya tsoro gami da taraddudi a zukatan najeriyawa cewa mene dalilin wannan magana a dai dai wannan lokaci d ake fatan samun zaman lafiya da kuma samun damar gudanar da zabe, abinda mutane ke cewa ”Idan babu rami me ya kawo rami?”
Ana fatan samun sauki daga wadannan tashe tashe ba hankulan kafin shekarar 2023 inda ake sa ran gabataar da zaben shugabancin kasar najeriya.
Kamar yadda kundin tsarin mulkin najeriya ya tanada hukumar INEC itace aka dorawa alhakin tabbatar da gudanuwarwar zabe cikin aminci da kwanciyar hankali, ba kuma tare da jinkiri wajen aiwatar da hakan ba.
Al’ummar najeriya sun zura idanu domin ganin yiwuwar zaben shekarar 2023 sakamakon matsin rayuwa, rashin tsaro gami da matsanancin tsadar rayuwa da ta addabi al’umma a loacin mulkin gwamnatin Baba Buhari wanda a da ake ma lakabi da mai gaskiya amma yanzu ga dukkan alamu wancan sunan babu shi.