Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya sake yin kira ga gwamnatin Najeriya da ta soke tallafin man fetur da kuma farashin canjin kudade na hukuma, tare da daukar matakan rage radadin da hakan zai haifarwa marasa karfi.
Wannan ba shi ne karo na farko da asusun IMF ke kira ga gwamnatin Najeriya kan bukatar cire tallafin mai kwata kwata ba, inda a baya bayan nan asusun ba da lamunin na duniya ya kara da bukatar soke da tsarin banbanta matakin canjin kudade na hukuma karkashin bankin CBN da kuma na bayan fage, ma’ana gwamnati ta kyale kasuwa ta fayyace darajar Nera.
Sai dai a yayin zantawar sa da sashin Hausa na RFI, Dr Kasim Garba Kurfi masanin tattalin arziki a Najeriya, ya ce bai yi mamakin kiran da IMF ya sake yi wa Najeriya ba, la’akari da cewar dole hakan ta faru ga kowace kasa da karbar bashi ya zamewa dole la’akari karin maganar da ke cewa ‘duk wanda ya ci ladan kuturu dole ya yi masa aski’
A bangaren bukatar maida kasuwar canjin kudaden kasashen ketare zuwa ta bai daya kuwa, Dr Kurfi ya ce matakin zai taimaka wajen kawo karshen karancin Dala a Najeriya, sai dai illar kuma da ke tattare da hakan itace dimbin bashin biliyoyin dalolin da ke kan kasar zai kusan ninka, da zarar an fara aiwatar da bukatar asusun lamunin na duniya.