Atiku Abubakar yakai yakin neman zabensa yankin Igbo a Nigeria, bayan zuwa jihar Anambra Atikun ya sauka a jihar Imo.
Atiku dai yace ƙabilar Igbo bata da wani dan takara wanda ya cancanta ace sun zaba sama dashi, domin shine yasan matsalar su kuma shi zai magance ta.
Atiku ya tabbatarwa da yan kabilar Igbo indai suna son su fitar da shugaban ƙasa daga cikinsu, to dole ne su mara masa baya, sabida shine tsaninsu.
Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubukar yace bai ga dalilin da ya inyamurai ba zasu zaɓi jam’iyyarsa ba.
Atiku na yin wannan maganar ne yayin yakin neman zabensa a dandalin Ndubusi Kanu da ke Owerrin Jihar Imo.
Rahotan jaridar Vanguard Dalilin Atiku na fadin haka bai wuce yadda ya zauna da ƴan kabilar Igbo yaji kukensu ba, da kuma buƙatunsu na san a sakewa Nigeria fasali.
Atikun yayi alƙawarin sa Dala Biliyan 10 dan bunƙasa kasuwancin yankin ƙabilar Igbo, sabida yadda aka san ƙabilar da kasuwanci “Idan kuka zaɓeni, to jihar Imo zata kasance ƴar gaban goshina.
Kun sani muna fama da matsalar tsaro a Imo da ma Nigeria gaba ɗaya.
“Idan kuka zaɓeni zan zauna da ku mu gano bakin matsalar kuma mu warwareta. Ina mu’amala da ƴan kabilar Igbo lokaci mai tsawo dan haka zanyi aiki da ku a gwamnatina in kuka zabeni.”
Tunda farko ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar PDP kuma gwamnan jihar Delta, Ifeanyi okowa yace: “Muna so kowa ya hada hannu damu dan ganin mun samu nasara a wannan yakin neman zaben. ”
Jam’iyyarmu ta tsayar da Atiku, sabida tasan shine kadai mutumin da zai iya kada ɗan takarar jam’iyyar APC”
“Ina fatan zamu aiki tare da ku dan kai jam’iyyar PDP ga Nasara Atiku Ya Fadawa Igbo Shine Tsaninsu”
A wani labarin kuma, Alhaji Atiku Abubakar ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP yace kabilar igbo bata da wani zabi na cikar burinta illa su mara masa baya.
Atikun na wannan maganar ne yayin da ya ziyarci jihar
Anambra yayim yakin neman zabensa. Atiku yace burin kabilar Igbo shine samar da shugaban kasa daga cikinsu to muddin suna son hakan su mara masa baya, domin shine tsanin su.