A firar da gidan talbijin na Press T.V suka gabatar dashi a jiya laraba babban shehin malamin nan, Sayyid Ibrahim Zakzaky ya bayyana cewa ”Idan aka bama ‘yan najeriya zabin tsarin da zai mulke su lallai zasu zabi tsain musulunci ne, kamar yadda aka bama iraniyawazabi kuma suka zabi tsarin musulunci” kuma zaban tsarin musulunci ya kawo musu cigba a bangarorin tsaro, tattalin arziki, jin dadin rayuwa da dai sauran su.
A firar sata farko tun bayan fitowar sa daga gidan kurkuku shehin malamin ya fara bada tarihin yadda harkar musulunci a najeriya ta soma da kuma yadda aka ta gamuwa da kalubale kala kala da kum yadda gwamnatoci suka dingi kokarin zaluntar mabiya wannan harkar ta musulunci.
Shehin malamin ya tabbatar da cewa idan abin a sanar ne sa ace lallai ita harkar musulunci bata takaita iya najeriya ba, a kwai mambobin harkar musulunci a sauran kasashen afirka irin su siera lionne da sauran su, dama sauran kasashen duniya a nahiyoyin asiya da europe.
Shehin malamin yayi nuni da yadda azzalumai sukayi kisan kare dangi a waqi’ar da ta faru a zariya a 12 ga disambar 2015, inda ya tabbatar da cewa wani bakin zalunci ne da kayi amma azzaluman basu iya cimma hadafin su na ruguza harkar ba illah ma cigaba da harkar tayi.
Da aka tambaye shi ko menen dalilin da yasa gwamnatin najeriya ke kaima almajiran sa hari alhali basu dauke da makami kuma basu da alamun nemna tada zaune tsaye, shehin malamin ya kada baki yace babu wani dalili wanda zamu iya fada domin suma masu kawo harin har zuwa yanzu sun kasa bada dalilan su na wannan zalunci da suke aiwatarwa.
Sai dai rahotanni sun tabbatar da hannun saudiyya a wasu daga cikin hare haren da ake kaiwa mabiya harkar musulunci wanda mafi yawancin su mabiya mazhabar shi’anci ne.
Ita saudiyya tana yakar harkar musulunci a najeriya ne domin tana ganin Jamahuriyar Mususulunci Ta Iran na samun tasiri da aringizon magoya baya a kullum a kasar ta najeriya dama afirka baki daya.