Tsohon jakadan Najeriya a Afrika ta Kudu, Musa Ibeto, ya yi murabus daga matsayin dan jam’iyyar APC a ranar Talata, 3 ga watan Janairu.
Ibeto ya yi ikirarin cewa APC a jihar Neja bata da hadin kai yayin da yawancin mambobinta basu nuna jajircewa ba yayin da ake fama da rikice-rikice a kotu.
Tsohon jigon na APC ya kuma bayyana barazanar cikin gida da rashin hobbasa don kaiwa ga nasarar jam’iyya a matsayinn dalilinsa na ficewa.
Daya daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Neja, Musa Ibeto, ya yi murabus daga jam’iyya mai mulki, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Ibeto, tsohon jakadan Najeriya a Afrika ta kudu, ya bayyana murabus dinsa daga APC a cikin wata wasika da ya gabatarwa shugaban APC a gudunmar Ibeto ta tsakiya a karamar hukumar Magama a ranar Talata, 3 ga watan Janairu.
Dalilin da yasa na bar APC, Ibeto Da yake bayyana dalilinsa a cikin wasikar, Ibeto ya yi ikirarin cewa jam’iyyar na fama da rashin hadin kai da rashin jajircewa a tsakanin mambobinta, jaridar The Nation ta rahoto.
Bugu da kari, Ibeto ya bayyana rikicin cikin gida da ya ki ci ya ki cinyewa, barazanar cikin gida da yiwa jam’iyya zagon kasa, da rashin sulhu na gaskiya a matsayin dalilinsa na ficewa daga jam’iyyar.
Jawabin na cewa: “Ya shugaba, da tsawon shekarun da na yi ina fafatawa a harkar siyasa kuma a matsayina na tsohon jigon jam’iyya, kuma zababben jami’i a mukaman siyasa daban-daban, na yanke wannan shawara ne saboda dalilai da dama; daga ciki akwai rashin hadin kai a tsakanin ‘ya’yan jam’iyya da masu ruwa da tsaki, barazanar cin dunduniyar jam’iyya, rashin sulhu na hakika da kuma rashin hobbasa don kaiwa ga nasarar jam’iyya a tsakanin masu ruwa da tsaki.
“Saboda wadannan dalilan, na yanke shawarar cewa ba zan iya ci gaba da zama dan jam’iyya ba. ”
Ya shugaba, da wannan murabus din nawa, na janye daga zama mamba a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Mataimakin Sakataren Kwamitin Yakin nema zaben APC na Arewa ta Tsakiya da dukkanin kwamiti da kungiyoyin jam’iyyar.”
Jigon kasa ya marawa takarar Peter Obi baya
A wani labari na daban, mun ji cewa babban jigon Najeriya, Cif Edwin Clark ya ayyana goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Peter Obi.
Clark ya ce Obi ne ya fi cancanta da shugabancin Najeriya don yana da halayen shugaba nagari.