Suleiman Othman Hunkuyi yace ya tafka kuskure da ya taimakawa jam’iyyar APC a zaben shekarar 2015.
Tsohon Sanatan Arewacin Kaduna yana nadamar ba Nasir El-Rufai da Muhammadu Buhari gudumuwa.
Jam’iyyar APC tayi wa Suleiman Othman Hunkuyi raddi, tace shi ne ya ci albarkacin Nasir El-Rufai a zabe.
‘Dan takarar Gwamnan jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar adawa ta NNPP, Suleiman Othman Hunkuyi ya dawo yana cizon yatsan sa.
Vanguard ta rahoto Suleiman Othman Hunkuyi a ranar 15 ga watan Nuwamba 2022, yana nadamar rawar da ya taka na daura APC a kan mulki.
Sanata Suleiman Othman Hunkuyi ya bayyana cewa ya yi kuskure da ya taimaka wajen kawo gwamnatin APC ga jihar Kaduna a zaben 2015.
Da yake bayani a wajen wani taron kungiyar kwadago na kasa watau NLC a Kaduna, Hunkuyi yace ya taimakawa APC a matakin jiha da na kasa.
An jefa Kaduna a ha’ula’i – Hunkuyi ‘Dan siyasar ya koka da halin da Kaduna ta shiga a yau, yace da farko bai yi niyyar cigaba da siyasa bayan 2019 ba, ya so ya koma gida ya huta.
A 2014, Hunkuyi yace ya yi tunanin Nasir El-Rufai zai dace da Gwamnan Kaduna, haka zalika Muhammadu Buhari kan kujerar shugaban kasa.
A ganin sa, kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba. ‘Dan siyasar yace wadanda aka zaba a APC sun jawo yayi nadama, wannan ya sa a zaben 2019 ya fadawa mutanen Kaduna ka da za su sake zabensu.
Hunkuyi bai taba cin zabe ba sai 2015 The Cable tace APC tayi martani, tace ‘dan siyasar bai taba cin zabe bayan zamansa shugaban karamar hukumar Makarfi a lokacin mulkin soja ba.
Za ayi wa Hunkuyi ritaya?
Darektan sadarwa na kwamitin yakin neman zaben APC, Ibraheem Musa ya fitar da jawabi a kan kalaman tsohon Sanatan na jihar Kaduna ta Arewa.
Ibraheem Musa yace Sanata Uba Sani zai dankara jam’iyyar NNPP da kasa a zaben 2023, kuma ya kawo karshen siyasar tsohon ‘dan majalisar kasar.
APC ta shiga matsala a Taraba An samu labari kotu tace zaben da APC ta shirya wanda aka ba Sanata Emmanuel Bwacha damar zama ‘dan takarar Gwamna a Taraba ya saba doka.
Kotu tayi umarni ga jam’iyyar APC tayi maza ta sake gudanar da zaben ‘dan takara wanda zai rike mata tutar Gwamnan jihar Taraba a zabe mai zuwa.
Source:LEGITHAUSA