Hukumomin Afrika ta kudu sun bayyana takaicinsu kan matakin dakatar da zirga-zirgar sufuri da kasar da wasu kasashe suka yi sakamakon bullar sabon nau’in cutar Korona mai suna Omicron.
Hukumar lafiya ta Duniya WHO dai ta bayyana matukar damuwa kan matakin da kasashen Duniya suka dauka na kule iyakokin su ga Afirka ta Kudu.
Kawo yanzu Biritaniya, Jamus da Italiya da kuma Jamhuriyar Czech suka tabbatar da bullar sabon nau’in cutar Koronar na Omicron a cikinsu, abinda ya sanya Amurka, da Canada da Australia shiga cikin jerin kasashen da suka dakatar da zirga-zirga tsakaninsu da Afirka ta Kudu a ranar Asabar, saboda gano sabon nau’in cutar Koronar na Omicron a kasar.
A wani labarin na daban ‘yan sandan Burkina Faso sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa daruruwan masu zanga-zangar adawa da gwamnati a babban birnin kasar a ranar Asabar.
Dandazon Jama’ar dai sun so su gudanar da zanga-zangar nuna adawa da gazawar shugaba Roch Marc Christian Kabore kan dakile tashe-tashen hankulan da ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi ke haddasawa da suka dabaibaye sassan kasar, amma kuma hukumomin tsaron suka dakile yunkurin.
Gamayyar kungiyoyin fararen hula uku ne suka shirya jagorantar zanga-zangar lumanar ta ranar Asabar din 27 ga watan Nuwamba, don yin tir da karuwar rashin tsaro tare da neman shugaba Kabore ya yi murabus.
Sai dai sauran kungiyoyin fararen hula sun nisanta kansu daga zanga-zangar, saboda a cewarsu, yin hakan zai iya jefa Burkina Faso cikin karin rudani.
Kungiyoyin da ke da alaka da Al-Qaeda da kungiyar IS mai da’awar kafa daular Islama sun addabi al’ummar kasar ta Burkina Faso da ke yankin Sahel tun daga shekara ta 2015, inda suka kashe mutane kusan dubu 2 tare da raba wasu akalla miliyan 1 da dubu 400 da gidajensu.
A wani hari da mayaka masu yawa suka kai a ranar 14 ga watan Nuwamba, kan wani sansanin Jandarma dake Inata a arewacin kasar, inda suka kashe ‘yan sanda 53 da wasu mutane hudu.