Hukumar shirya zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta sanar da ranar da za’a gudanar da zaben shugaban kasa, yan majalisa da gwamnoni na shekarar 2023.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya sanar da hakan a hira da manema labarai ranar Asabar a birnin tarayya Abuja.
A cewarsa, za’a gudanar da zaben Shugaban kasa da na majalisar dokokin tarayya ranar Asabar, 25 ga watan Febrairu, 2023.
Yayinda na gwamnoni da majalisar dokkin jiha zasu gudana ranar Asabar, 11 ga Maris, 2023. Yakubu yace wannan sabon rana ya yi daidai da ka’idojin da doka ta gindaya na sanar da ranar zabe ana saura akalla kwanaki 260 da ranar zabe.
A wani labarin na daban kuma Akalla mutane sama da 500 suka shiga zanga zangar adawa da gwamnatin sojin Chadi a birnin Ndjamena, yayinda su ke sukar kasar Faransa da su ke zargin cewar ta na daurewa jagorancin Sojin kasar gindi.
Masu zanga zangar suna dauki allunan da ke nuna cewar, ‘a kawo karshen cin zarafin da Yan Sanda ke yi’, ‘Faransa ta fita a Chadi’, yayin da suke fadin ‘Bamu yarda da Faransa ba’, ‘muna goyan bayan Rasha’ da kuma ‘muna bukatar Rasha kamar yadda take a Mali.
Kamfanin dillancin labaran Faransa yace an ga matasa na jan tutar Faransa a kasa daga cikin mota da kuma taka ta, yayin da wasu ke daga tutar Rasha da Chadi.
Max Loalngar, mai magana da yawun Wakit Tamma ya bayyana cewar sojoji ne suka haifar da matsalar Chadi lokacin da ya ke magana da taron mahalartar zanga zangar, yayin da yayi zargin cewar Faransa na hada baki da sojin wajen hallaka su.
Masu zanga zangar sun kuma bukaci gudanar da taron kasa na gaskiya wanda zai kaiga lalubo hanyar warware rikicin kasar.