Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Najeriya EFCC, ta cafke tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano.
An tsare tsohon gwamnan ne ‘yan lokota bayan da ya mika mulki ga Charles Soludo,tsohon gwamnan babban bankin Najeriya.
A watan nuwamba na shekarata 2021 ne hukumar EFCC ta mika wasika ga hukumar shige da fice ta kasa na ganin ta sanar da ita a duk lokacin da Willie Obiano ke yunkurin ficewa daga kasar.
A wani labarin mai kama da wannan daga birnin kano, Rahotanni daga jihar Kano a Tarayyar Najeriya na cewa jami’an hukumar EFCC sun kame mai dakin gwamnan jihar Hajiya Hafsat Umar Ganduje bayan da ta ki amsa gayyatar da hukumar ta yi mata dangane da badakalar wani fili tsakaninta da danta.
Kamen na zuwa makwanni bayan wa’adin da hukumar ta EFCC ta dibar mata don bayyana gabanta game da takaddamar wadda danta Abdul’aziz Ganduje ya shigar da korafi gaban hukumar don nemar masa hakkinsa.
Tun a ranar 23 ga watan Satumba da ya gabata, hukumar ta EFCC ta bukaci Hajiya Hafsat ta bayyana gabanta amma kuma matar Gwamnan na Kano Abdullahi Ganduje ta ki mutunta gayyatar, ko da ya ke wata makusanciyarta ta shaidawa manema labarai cewa a lokacin mai dakin gwamnan na kasar Birtaniya.
Wasu bayanai daga gidan gwamnatin jihar ta Kano na cewa tun a yammacin jiya litinin jami’an hukumar suka kame Hajiya Hafsat Ganduje, sai dai babu cikakken bayani kan ko ta dawo gida ko kuma tana ci gaba da fuskantar dauri a hukumar gabanin fara sauraron bahasi kan korafin.
Tun farko Abdul’aziz Ganduje ne ya fara kaiwa EFCC batun don ganin hukumar ta shiga tsakani don kwatar masa hakkinsa da ya ce mahaifiyartasa na kokarin yi masa sama da fadi akai.
Bayanai sun ce almundahana da rashawa sun dabaibaye lamarin filin tsakanin Hafsa Ganduje da dan nata Abdul’aziz.
Wannan dai ba shi ne karon farko da Iyalan gwamnan na Kano ke tsintar kansu a lamurra masu alaka da cin hanci rashawa ko kuma almundahana ba, la’akari da cewa shi kansa Gwamnan akwai zarge-zarge da suka dabaibaye tsarin tafiyar da mulkinsa.